"Mun Bada Shi Aro," PDP Ta Yi Magana game da Alakar Nyesom Wike da Jam'iyyar APC

"Mun Bada Shi Aro," PDP Ta Yi Magana game da Alakar Nyesom Wike da Jam'iyyar APC

  • PDP ta ce ba za ta bari Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya koma APC har abada ba, tana mai cewa har yanzu shi ne babbar kadar jam'iyyar
  • Jam’iyyar ta bayyana cewa Wike yana tare da gwamnatin APC a matsayin 'aro', kuma zai koma PDP bayan kammala aikin da aka ba shi
  • Martanin PDP ya zo ne bayan shugaban APC ya yaba da ayyukan Wike a matsayin minista da kuma rawar da yake takawa a gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa babu wani shiri da zai sanya Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya koma jam’iyya mai mulki ta APC gaba daya.

Jam’iyyar ta ce tana kallon Wike, wanda ke aiki a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, a matsayin "dan aro” domin gudanar da wani aikin kasa, kuma zai koma PDP bayan kammala wannan aiki.

Kara karanta wannan

Bayan mutuwar jigo a Izala, tsohon shugaban APC ya rasu a hannun yan bindiga

PDP ta ce Wike ba zai taba komawa APC ba.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike a dakin taron FCTA. Hoto: @GovWike
Source: Twitter

Martanin PDP ga shugaban APC

Wannan martani na PDP ya biyo bayan kalaman Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, wanda ya yaba wa ayyukan Wike a matsayin ministan Abuja, in ji rahoton Tribune.

Yilwatda ya yi wannan jawabi ne yayin kaddamar da sababbin ayyuka a Abuja, inda ya nuna jin dadinsa kan irin sauye-sauyen da Wike ya kawo a babban birnin tarayya.

Sai dai PDP ta mayar da martani inda ta ce kalaman shugaban APC ba su nufin cewa Wike zai koma jam’iyyar APC na dindindin ba.

'Wike ba zai koma APC ba' - PDP

Sakataren Yada Labarai na PDP na kasa, Jungudo Haruna Mohammed, ya bayyana cewa kasancewar Wike a gwamnatin APC ba yana nufin an yi wani shirin canja masa sheka ba.

Jam’iyyar ta ce:

“Ana iya bayyana shigar Wike cikin gwamnatin APC a matsayin wani tsari na aro, kuma muna tabbatar da cewa babu wata yarjejeniya da ta tanadi canja wurinsa gaba daya.”

Kara karanta wannan

2027: Kwankwaso ya tsallake NDC, ya sayi fam din takara a jam'iyyar PRP? Gaskiya ta fito

Jaridar Punch ta rahoto PDP ta kara da cewa ba ta da niyyar rabuwa da daya daga cikin muhimman jiga-jiganta na siyasa.

PDP ta kare matsayin Wike

Jam’iyyar ta bayyana Wike a matsayin daya daga cikin manyan kadarorinta na siyasa, tana mai cewa ba ta da wani shiri ko tattaunawa da zai kai ga barinsa ya koma APC.

PDP ta ce ba ta da aron Wike ne kawai don yi wa kasa hidima.
Ministan Abuja, Nyesom Wike yana jawabi a wani taro da aka shirya lokacin yana Gwamnan Rivers. Hoto: @GovWike
Source: Facebook

Ta gargadi APC da kada ta yi tsammanin samun Wike a matsayin dan jam’iyyar ta na dindindin, tana mai cewa za ta yi tsayin daka wajen kare matsayinsa a PDP.

PDP ta ce aikin Wike a gwamnatin APC bai sauya matsayinsa na siyasa ko rage irin gudunmawar da ya bayar wajen karfafa PDP ba.

Jam’iyyar ta ce har yanzu tana daraja rawar da tsohon gwamnan Rivers ya taka a siyasarta tsawon shekaru.

Wike ya tabo batun shiga APC

A wani labari, mun ruwaito cewa, Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi tsokaci kan yiwuwar ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki.

Nyesom Wike ya bayyana cewa ficewar da wasu ke yi zuwa APC, ba za ta sanya ya raba gari da jam'iyyar PDP ba.

Ministan na Abuja ya nuna cewa jam'iyyar PDP za ta shiga tsaka mai wuya duk lokacin da ya yanke shawarar barinta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com