Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Mataimakin kakakin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Yekini Nabena ya zargi Alhaji Atiku Abubakar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da shirin hargitsa kasar gabannin zaben Shugaban kasa na 2019.
Kasa da makonni biyu kafin zaben ranar 16 ga watan Fabrairu, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), ta tsawaita ranar karban katunan zabe na karshe inda ta mayar dashi zuwa ranar Litinin, 11 ga watan Fabrairun 2019.
Mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dama a jihar Akwa Ibom sun koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Daya daga cikin masu sauya shekar shine tibe Ibanga, wani hadimin Gwamna Udom Emmnuel.
Tsohuwar ministar kasuwanci a karkashin gwamnatin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, Misi Josephine Tapgun ta sauya sheka daga jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).
Buba Galadima, kakakin kungiyar kamfen din dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya bayyana cewa dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar zai lallasa Shugaban kasa Buhari a zabe.
Dan takarar kujerar sanata a PDP, Mustafa Sule Lamido, ya bayyana cewa ya samu karin karfin guiwar fitowa takara sakamakon amincewa da dokar ba matasadamar yin takara wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba ma hannu.
Wata yarinya yar shekara tara mai suna Gassana Aliyu na layin Kasarau Yamma da ke Dutse, babbar birnin jihar Jigawa ta hadu da ajalinta sakamakon fadawa da tayi cikin wata rijiya. Lamarin ya afku ne da misalin karfe 1:30 na rana.
Rahotanni da ku zuwa mana sun nunacewa hukumar kula da albarkatun man fetur ta fitar da sanarwan cewa gobe Asabar 2 ga watan Fabrairu, shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da sabbin rijiyoyin men fetur da aka samu a Bauchi.
Kubuwa wata nauyin kayan lambu ne da akan yi amfani wajen yin miya. Mutane da dama na miyar kubewa saboda dadinta ne kawai amma ga kadan daga cikin amfaninta a matsayin magani wanda aka shafe shekaru dauruwa ana amfani da ita.
Aisha Musa
Samu kari