Jam’iyyar AD ta yi watsi da Buhari ta mara wa Atiku baya a matsayin dan takarar shugaban kasa

Jam’iyyar AD ta yi watsi da Buhari ta mara wa Atiku baya a matsayin dan takarar shugaban kasa

Kasa da sa’o’i 24 zuwa zaben shugaban kasa na ranar 16 ga watan Fabrairu, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya samu babban garkuwa yayinda jam’iyyar Alliance for Democratic (AD) mara masa baya.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa hukuncin goyon bayan Atiku ya biyo bayan ganawar da jam’iyyar tayi a Abuja inda ta saki jawabanta ga manema labarai a ranar Alhamis, 14 ga watan Fabrairu.

Legit.ng ta tattaro cewa sanarwar goyon bayan PDP na dauke da sa hannun shugaban kungiyar na yankin kudu maso yamma, Otunba Tayo Onayemi.

Jam’iyyar AD ta yi watsi da Buhari ta mara wa Atiku baya a matsayin dan takarar shugaban kasa

Jam’iyyar AD ta yi watsi da Buhari ta mara wa Atiku baya a matsayin dan takarar shugaban kasa
Source: UGC

Jam’iyyar tace ta mara wa Atiku baya ne saboda tayi amanna cewa dan takarar na PDP na da kwarewa daban-daban a gwamnati, duba ga cewar ya taba rike mukamin mataimakin shugaban kasa na tsawon shekaru takwas.

KU KARANTA KUMA: Masu ritaya 243,166 sun karbi N7.82bn a matsayin fansho cikin watan Janairu kacal

Jam’iyyar ta kuma kara da cewa alkawarin sake fasalin kasar da dan takarar shugaban kasa na PDP yayi ne ya kara basu karfin gwiwar mara masa baya.

A wani lamari na daban, mun ji cewa Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tana zargin babban jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) da bawa masu ruwa da tsaki a harkar zabe cin hanci domin su ba su fifiko.

A cikin sanarwar da kakakin jam'iyyar APC na kasa, Lanre Issa-Onilu ya fitar ya ce jam'iyyar adawan tana aikata hakan ne saboda tana tsoron shan kaye a zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel