Yarinya yar shekara 9 ta nitse cikin rijiya a jihar Jigawa

Yarinya yar shekara 9 ta nitse cikin rijiya a jihar Jigawa

- Yarinya yar shekara tara mai suna Hassana Aliyu ta hadu da ajalinta sakamakon fadawa da tayi cikin wata rijiya

- Babu wani takamaiman bayani kan yadda aka yi ta fada a rijiyan da ke gidansu

- Tawagar bayar da agaji sun yi gaggawan fito da ita amma ko da aka je asiti rai yayi halinsa

Wata yarinya yar shekara tara mai suna Hassana Aliyu na layin Kasarau Yamma da ke Dutse, babbar birnin jihar Jigawa ta hadu da ajalinta sakamakon fadawa da tayi cikin wata rijiya.

Alhaji Ahmed Danyaro, daraktan hukumar kashe gobara na jihar Jigawa ya sanar da kamfanin dillancin labaran Naeriya (NAN) a garin Dutse a ranar Juma’a cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 1:30 na ranar Alhamis.

Yarinya yar shekara 9 ta nitse a rijiya a jihar Jigawa

Yarinya yar shekara 9 ta nitse a rijiya a jihar Jigawa
Source: Twitter

Danyaro yace: “Babu wanda zai iya bayyana yadda akayi marigayiyar ta fada cikin rijiyar kamar yadda muka samu labara ance ta fada cikin rijiyan ne a gidansu.

“Da samun labarin lamarin, sai muka yi gaggawan tura tawagar ceto wadanda suka ceto ta cikin mawuyacin hali sannan daga bisani aka tabbatar da mutuwarta a asibiti."

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kai farmaki ga tawagar 'yan sanda, sun kashe ASP a Delta

Yace tuni aka mika gawar marigayiyar ga iyayenta domin binneta.

Ya kuma shawarci iyayen da ke da rijiy a gidajensu da su kara tsawonsa sannan su samar da murafen rijiya dmin kare yayansu da yankunan.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel