Amfanin kubewa guda 5 a jikin Dan Adam

Amfanin kubewa guda 5 a jikin Dan Adam

Kubuwa wata nauyin kayan lambu ne da akan yi amfani wajen yin miya. Hasashe sun nuna cewar Kubewa ta samo asali ne daga kasar Habasha wato Ethiopia da kuma Masar wato Egypt tun karni na 12.

Mutane da dama na shan miyar kubewa don dandano da dadinta ne kawai ba tare da sanin tarin alfanun da ke tattare da ita ba.

Hakan yasa muka binciko maku kadan daga cikin amfaninta a matsayin magani ga garkuwar jikin Dan Adam.

Amfanin kubewa guda 5 a jikin Dan Adam
Amfanin kubewa guda 5 a jikin Dan Adam
Asali: UGC

Ga su nan kamar haka:

1. Ana amfani da kubewa wajen maganin cutar siga wacce ta zamo ruwan dare a tsakanin al'umma a yanzu. Tana dauke da sinadarin fibre a cikinta, wanda ke taimakawa wajen daidaita yawan siga a cikin jikin dan Adam, wanda kuma ke rage karfi ciwon siga ko ma maganinsa.

2. Kubewa na matukar tallafa wa masu juna biyu wajen inganta lafiyarsu da kuma na jaririn da ke ciki domin kubewa na kunshe da dimbin Vitamin B da ke samarwa da kuma inganta sabbin kwayoyin halitta na gina jiki da. lafiyarsa.

3. Ta na kuma maganin cutar wahala wajen fitar da numfashi wato Asthma, saboda sinadarin Vitamin C da ke tattare ta ita.

KU KARANTA KUMA: APC ta bijire wa INEC, ta sha alwashin cike yan takara a Zamfara da Rivers

4. Ga mai son kara inganta fatan jikin sa ya yi laushi da santsi kamar yaukin kubewar toh ya lazumci amfani da ita.

5. Yana matukar maganin karancin jini a jiki domin kubewa na kunshe da sinadarin Iron sosai. Kuma yawan amfani da kubewa na sanya idan ka ji rauni jini ba zai zuba da yawa har ya yi wa mutum lahani ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng