Abba zai Kafa Hukumar Gidaje don Magance Tsadar Kudin Haya a Kano

Abba zai Kafa Hukumar Gidaje don Magance Tsadar Kudin Haya a Kano

  • Gwamnatin Jihar Kano ta fara shirin kafa hukumar kula da harkokin gidaje domin dakile tashin gwauron zabin kuɗin haya da sauran matsaloli a ɓangaren gidaje
  • Kwamishinan gidaje na jihar, Ibrahim Yakubu-Adamu, ya ce tuni aka aika da takardar neman amincewar Gwamna Abba Kabir Yusuf kan kafa hukumar
  • Ya bayyana cewa hukumar za ta sa ido kan masu harkar gidaje tare da magance abubuwan da ke haddasa tsadar haya a jihar Kano baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano – Gwamnatin Jihar Kano ta fara shirin kafa hukumar kula da harkokin gidaje domin daidaita yadda ake gudanar da kasuwancin gidaje, tare da dakile tsadar kuɗin haya da sauran matsaloli a ɓangaren.

Kwamishinan Ma’aikatar Bunƙasa Gidaje ta jihar, Arc. Ibrahim Yakubu-Adamu, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Laraba, jim kaɗan bayan kare kasafin kuɗin ma’aikatar na shekarar 2027 a gaban majalisar dokokin jihar.

Kara karanta wannan

An jero mutanen da za su yi wa Sarkin Daura titsiye kan zargin taba baturiya

Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf. Hoto: Sanusi Bature
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa kwamishinan ya ce ma’aikatar ta aika da takardar neman amincewar Gwamna Abba Kabir Yusuf domin kafa hukumar, amma har yanzu tana jiran amincewarsa.

Yadda sabuwar hukumar za ta yi aiki

Yakubu-Adamu ya ce hukumar da ake shirin kafawa za ta kula da ayyukan masu harkar gidaje, tare da dakile abin da ya kira wuce gona da iri da wasu ke yi a ɓangaren.

Ya bayyana cewa matakin zai taimaka wajen magance wasu ayyuka da ke haddasa tsadar kuɗin haya a jihar Kano.

Kwamishinan ya ce:

“Mun aika wa mai girma gwamna takarda domin kafa sashen kula da harkokin gidaje ko hukumar da za ta kasance ƙarƙashin Ma’aikatar Bunƙasa Gidaje. Ana kan aiwatar da shirin, kuma ina fatan gwamna zai amince da shi.”

Ana shirin kafa hukumar ƙasa

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa Majalisar Dokoki ta Ƙasa na duba yiwuwar kafa hukumar ƙasa da za ta kula da harkokin gidaje a faɗin Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamna ya karɓi rahoton abubuwan da aka gano kan mutuwar matasa 37 a ofishin NSCDC

Ya ce kusan mako biyu da suka gabata, ofishin shugaban majalisar da shugaban kwamitin majalisar kan gidaje da muhalli, Abdulmumini Jibril-Kofa, sun gayyaci ma’aikatar domin tattaunawa kan kudirin dokar.

A cewarsa, hukumar da ake shirin kafawa za ta taimaka wajen sa ido kan harkokin gidaje da kuma dakile duk wani abu da bai dace ba a ɓangaren.

Taswirar jihar Kano
Taswirar jihar Kano a Najeriya.
Source: Original

Da yake magana kan shirye-shiryen ma’aikatar na shekarar 2027, Yakubu-Adamu ya ce za a ba da fifiko wajen ci gaba da ayyukan gidajen da aka fara a sassan jihar.

Barau ya tara malamai a Kano

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Barau Jibrin ya nemi goyon bayan malaman addinin Musulunci sama da 2,000 daga Kano ta Arewa.

Barau ya bayyana ayyukan raya ƙasa da gwamnatin tarayya ta kawo Kano, yana mai cewa Shugaba Bola Tinubu na da niyyar kawo ci gaba ga jihar.

Sanatan ya kuma sanar da shirin rabon babura 390 da tallafin N50,000 ga kowane malami domin tallafa musu a ƙananan hukumomi 13.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng