Buhari zai kaddamar da rijiyoyin man fetur da aka samu a jihar Bauchi

Buhari zai kaddamar da rijiyoyin man fetur da aka samu a jihar Bauchi

Rahotanni da ku zuwa mana sun nunacewa hukumar kula da albarkatun man fetur na kasa (NNPC) ta fitar da sanarwan cewa gobe Asabar 2 ga watan Fabrairu, shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da sabbin rijiyoyin men fetur da aka samu nasaran tonawa a jihar Bauchi.

An dai yi nasarar tono man ne a yankin kogin Kolmani dake karamar hukumar Alkaleri na jihar Bauchi.

Wannan shine karo na farko a tarihin duniya da aka yi nasarar tona rijiyoyin man fetur a yankin arewa.

Buhari zai kaddamar da rijiyoyin man fetur da aka samu a jihar Bauchi

Buhari zai kaddamar da rijiyoyin man fetur da aka samu a jihar Bauchi
Source: Twitter

Wannan babban nasara da aka samu ya sa jihar Bauchi za ta shiga jerin jihohi masu arzikin man fetur a Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Kiristoci sun yi wa Shugaba Buhari wa'azi mai ratsa zuciya

A wani lamari na daban, Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yayi alkawarin karasa gadar Niger ta biyu matukar aka zabe shi.

Atiku, wanda yayi alkawarin a jiya yayi babban zagayen kamfen din shi a Onitsha, yace zai tabbatar da an gaggauta kammala gadar saboda matarshi daga birnin kasuwancin jihar Anambra take.

Yayi alkawarin tabbatar da kammaluwar tare da gyara tituna a yankin da taimakon mataimakin shi, Mr Peter Obi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel