Adam A. Zango ya bar tafiyar Atiku ya sake komawa ta Buhari

Adam A. Zango ya bar tafiyar Atiku ya sake komawa ta Buhari

Labari da ke zuwa mana a yanzu ya nuna cewa shahararren jarumin nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood kuma mawakin zamani, Adam A. Zango ya fice daga tafiyar dan takarar Shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar sannan a karo na biyu ya sake komawa APC.

Shafin Rariya ta rahoto cewa jarumin wanda ya kasance masoyin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin barinsa APC yace shaidan ne ya rude shi har ya bar tafiyar Buhari.

Tun farko dai da jarumin ya sanar da komawarsa PDP ya fuskanci suka da matsi daga wajen wasu masoyansa dama wasu daga cikin abokan sana’arsa yayinda wasu ke ganin yana da yancin yin haka.

Adam A. Zango ya bar tafiyar Atiku ya sake komawa ta Buhari
Adam A. Zango ya bar tafiyar Atiku ya sake komawa ta Buhari
Asali: UGC

Ya dai bayyana dalilin barinsa tafiyar Buhari tun farko ya samo asali ne ga yadda abokan harkarsa ke nuna masa wariya da son kai wajen gudanar da lamuran jam’iyyar reshen Kannywood.

KU KARANTA KUMA: Ikon Allah ne kada zai iya hana zabe a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu – Shugaban INEC ga kasashen duniya

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Adam A. Zango ya karyata cewa wai wasu fusatattun matasa sunyi masa duka a garin Kano domin ya 'zagi' Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wasu mutane sun rika yadawa a kafafen sada zumunta a ranar Alhamis cewa an kwantar da Zango a asibiti bayan wasu 'yan daba sun lakada masa duka saboda ya fice daga cikin jerin magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari ya koma goyon bayan dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel