Abin Tausayi: An Kashe Mutane 5 Suna cikin Barci da Tsakar Dare a Jihar Jigawa
- Mutane biyar sun mutu, wasu shida kuma sun samu raunuka a wani harin ramuwar gayya da aka kai kauyen Gurjiya da ke jihar Jigawa
- Hukumar tsaro ta NSCDC ta ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare ranar Laraba, 25 ga Nuwamba, 2026
- An fuwaito cewa jami’an tsaro sun isa yankin domin gano waɗanda ake zargi da kai harin tare da cafke su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jigawa, Nigeria - An tabbatar da mutuwar mutane biyar, yayin da wasu shida suka samu raunuka daban-daban bayan wasu da ake zargin gungun ɓarayi ne suka kai harin ramuwar gayya a jihar Jigawa.
Lamarin ya faru ne a kauyen Gurjiya da ke gundumar Aujara, ƙaramar hukumar Jahun a jihar Jigawa.
Leadership ta rahoto cewa mai magana da yawun hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC), reshen jihar Jigawa, ASC Badruddeen Tijjani Mahmud, ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamba, 2026.
A cewarsa, waɗanda ake zargin ɓarayin ne daga wani matsugunin makiyaya, sun taɓa ƙoƙarin shiga kauyen watanni biyu da suka gabata. A lokacin, an kashe ɗaya daga cikinsu, yayin da wani ya samu rauni.
Sai dai a wannan karon, mutanen sun kai wa kauyen hari ne ba zato ba tsammani.
Sunayen waɗanda suka mutu
Badruddeen ya bayyana sunayen mutanen biyar da suka rasa rayukansu a harin kamar haka:
- Abdulmumini Abdullahi, mai shekara 70
- Malam Ashiru, mai shekara 70
- Miko Maigwanjo Duja, mai shekara 60
- Aki Faruq Atman, mai shekara 45
- Isyaku Imamu, mai shekara 50
Ya kuma bayyana cewa an garzaya da waɗanda suka samu raunuka zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.
Daga cikin waɗanda suka jikkata akwai Bala Idris, mai shekara 40, daga kauyen Taraya, da Alhaji Ado Usaini, mai shekara 60, wanda rahotanni suka ce an same shi a sume.
An tura jami’an tsaro yankin
Mai magana da yawun NSCDC ya bayyana cewa an tura haɗin gwiwar jami’an tsaro zuwa yankin domin shawo kan lamarin.
Ya ce jami’an tsaron suna aiki tare da shugabannin al’umma domin gano waɗanda ake zargi da aikata ta’asar tare da cafke su.
A cewarsa, matakin na daga cikin ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, bayan harin da ya jawo asarar rayuka da jikkatar wasu mazauna kauyen.
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng

