‘Yan bindiga sun sake bude wa mutanen Peter Obi wuta wajen yakin zabe a jihar Edo

‘Yan bindiga sun sake bude wa mutanen Peter Obi wuta wajen yakin zabe a jihar Edo

  • Wasu ’yan bindiga sun buɗe wa jama’a wuta a wani gangamin Peter Obi wuta wajen yakin zaben jam’iyyar NDC a Benin
  • ’Yan sandan reshen jihar Edo sun ce sun fara farautar maharan, tare da ƙara jami’an tsaro a wurin da wannan lamari ya faru
  • Harin ya zo ne kwanaki kaɗan bayan kashe mutane a taron NDC a jihar Delta, jami’ai sun yi alwashin za su yi bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Edo - Rundunar ’yan sandan jihar Edo ta ce ta ƙara ƙaimi wajen kamo wasu ’yan bindiga uku da suka buɗe wa jama’a wuta wajen kamfe.

Sun yi ta’adin ne yayin wani gangamin siyasa na ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, a birnin Benin a ranar Laraba.

Premium Times Rundunar ta shaida cewa maharan sun zo wurin ne cikin wata motar Toyota Hilux mai launin baƙi, suka buɗe wa mutane wuta.

Hakan ta faru bayan arba da jami’an ’yan sanda da aka girke a ƙofar fita ta filin jirgin saman Benin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tarfa mutanen gari da daddare, sun kashe mata, yara da matasa da dama

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Eno Ikoedem, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a birnin Benin kuma ana kan bincike.

ASP Eno Ikoedem ta ce maharan sun canza hanya bayan sun hango jami’an ’yan sandan, sannan suka buɗe wuta kafin su tsere daga wurin.

Ta ce wani mutum mai suna Aimionkhale Micheal ya samu rauni daga harbin bindiga a cinyoyinsa, don haka aka garzaya da shi zuwa wani asibiti.

A cewar kakakin, kwamishinan ’yan sandan jihar Edo, Patrick Daaor, ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, daga bisani kuma ya je duba shi a asibiti.

Ta ce kwamishinan ya kuma tura ƙarin jami’an tsaro zuwa wurin gangamin da asibitin domin hana sake kai wasu hare-hare in ji jaridar Vanguard.

Ikoedem ta ce an tura jami’an sashen yaƙi da manyan laifuffuka da sauran dakaru na musamman zuwa wurare daban-daban domin gano maharani.

Ta ce kwamishinan ya umarci mataimakin kwamishinan ’yan sanda mai kula da sashen binciken manyan laifuffuka na jihar ya yi cikakken bincike.

Kakakin ’yan sandan ta ce rundunar ta yi Allah-wadai da harin, tare da gargaɗin mutane da ƙungiyoyi da su guji duk abin da zai jawo rikici.

Kara karanta wannan

Mahara sun bude wuta kan magoya bayan NDC bayan isowar Kwankwaso da Peter Obi

Haka zalika an buƙaci mazauna jihar da su kwantar da hankulansu, su ci gaba da yin harkokin yau da kullum, suna masu taimaka wa jami’an tsaro.

Ta tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ɗauki duk matakan da suka dace domin kamo waɗanda suka aikata wannan aika-aika kan mutanen Obi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng