"Babban Kalubalen da Peter Obi da Kwankwaso Za Su Fara Tunkara idan Suka Ci Zaben 2027"

"Babban Kalubalen da Peter Obi da Kwankwaso Za Su Fara Tunkara idan Suka Ci Zaben 2027"

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi gwamnatin APC da gaza shawo kan matsalolin Najeriya, musamman rashin tsaro da matsin rayuwa
  • Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC ya ce jam’iyyarsa na da tsare-tsaren da za su inganta rayuwar ’yan Najeriya
  • Kwankwaso ya yi alƙawarin cewa gwamnatin NDC za ta yi ƙoƙarin rage farashin man fetur da sauran makamashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar NDC ta yi alƙawarin ceto ’yan Najeriya daga ƙalubalen tattalin arziki da rashin tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ne ya fadi hakan, inda ya zargi gwamnatin APC mai mulki da gaza wa.

Kwankwaso.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Tsohon gwamnana Kano ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da Leadership Hausa a Abuja cikin wannan mako.

Kara karanta wannan

Hare hare kan Obi, Kwankwaso ya fara tono boyayyun abubuwa, NDC ta yi gargadi

Kwankwaso ya afadi tsare-tsaren NDC

Kwankwaso, wanda shi ne jagoran tafiyar siyasar Kwankwasiyya ya ce NDC ta samar da tsare-tsare da shirye-shiryen da za su iya magance matsalolin ƙasar ta hanyar shugabanci na gaskiya, adalci da kula da muradun jama’a.

Ya nuna kwarin gwiwar cewa gwamnatin da Peter Obi zai jagoranta a matsayin shugaban ƙasa, shi kuma a matsayin mataimakinsa, za ta dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.

Tsohon gwamnan jihar Kano ya yi kira ga ’yan Najeriya da su haɗa kai su mara wa NDC baya, tare da kaɗa ƙuri’unsu domin kawar da APC daga mulki a zaɓe mai zuwa.

Ya ce ƙasar na buƙatar sauyin shugabanci cikin gaggawa domin magance matsalolin rashin tsaro, raguwar ingancin ilimi da kuma tsadar rayuwa.

Ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnatin NDC za ta yi aiki domin rage farashin man fetur da sauran kayayyakin makamashi.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: NDC ta tsoma baki kan zarge zargen da Gwamna Abba ya ɗorawa Kwankwaso

Kalubalen da NDC za ta fara warwarewa

Kwankwaso, wanda ya taɓa riƙe muƙamin Ministan Tsaro, ya ce yana mamakin yadda matsalar tsaro ta ƙara tabarbarewa a Najeriya.

Ya ƙara da cewa ’yan ƙasar na cikin mawuyacin hali, inda da dama ke rayuwa cikin fargaba da damuwa.

Ya bayyana rashin tsaro a matsayin babban ƙalubalen farko da gwamnatin Obi da Kwankwaso za ta fara magancewa idan ta karɓi mulki.

A cewarsa, bayan an dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali, gwamnatin za ta mayar da hankali kan inganta harkar ilimi.

Peter Obi da Kwankwaso.
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi da mataimakinsa, Sanata Rabiu Kwankwaso a babban gangamin jam'iyya a Abuja Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Ya ce matsalar rashin tsaro ta shafi kusan dukkan fannoni na tattalin arziki da rayuwar al’umma, ciki har da ilimi, samar da ababen more rayuwa, samun ruwan sha mai tsafta, gina hanyoyi da kuma noma.

Kwankwaso ya bayyana cewa babu wani ɓangare da zai iya gudanar da ayyukansa yadda ya kamata ba tare da isasshen tsaro ba. Saboda haka, ya ce magance matsalar tsaro ce za ta zama babban fifikon gwamnatin tasu bayan kama aiki.

Kara karanta wannan

APC ta maida martani ga matasan Arewa da suka ce ba za su zaɓi Tinubu a 2027 ba

An kai korafin Kwankwaso ga EFCC

Kun ji cewa wuta ƙungiyar farar hula ta roƙi EFCC ta binciki kadarori 10 da ta ce ana danganta su da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Kungiyar SACGGI ta nemi EFCC ta tantance masu wadannan kadarori da kuma tushen kuɗin da aka yi amfani da su wajen sayensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262