Tinubu Ka Iya Rasa Muhimmiya Jiha a Arewa kan Rigimar Gwamna da Manyan Kasa

Tinubu Ka Iya Rasa Muhimmiya Jiha a Arewa kan Rigimar Gwamna da Manyan Kasa

  • Terwase Orbunde ya gargaɗi cewa Shugaba Bola Tinubu na iya rasa gagarumin goyon bayan al'ummar Benue a zaɓen 2027
  • Ɗan takarar gwamnan Benue ya zargi Gwamna Hyacinth Alia da kawo cikas ga ƙoƙarin sasanta rikicin
  • Orbunde ya buƙaci shugabannin APC na ƙasa su aiwatar da hukuncin kotu, su haɗa kan jam’iyyar tare da tabbatar da dimokuraɗiyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Makurdi, Benue - Wanda ya nemi takarar kujerar gwamnan jihar Benue a jam’iyyar APC, Terwase Orbunde, ya gargaɗi Bola Tinubu.

Ortunde ya bayyana cewa Tinubu na iya rasa goyon bayan masu zaɓe a jihar a zaɓen 2027 idan ba a warware saɓanin da ke tsakanin Gwamna Hyacinth Alia da Sanata George Akume ba.

Ana rikici a tsakanin manyan yan APC
Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume. Hoto: Senator George Akume.
Source: Facebook

Ana zargin gwamna da ruruta rikicin APC

Orbunde ya bayyana cewa ƙoƙarin da ake yi na sasanta ɓangarorin biyu a APC ta jihar ya gaza tun farko, yana zargin Gwamna Alia da kawo cikas ga matakan da ake dauka na kawo maslha, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nuna damuwa kan ɗalibai 78 da aka sace, ya ɗauki alƙawari mai girma

Ya kuma zargi gwamnan da yin watsi da hukuncin kotuna kan tsarin shugabancin jam’iyyar a jihar.

Da yake jawabi yayin taron manema labarai na duniya a Abuja ranar Laraba, tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnan Benue ya ce Tinubu na da dimbin magoya baya a jihar waɗanda ba su cikin tsarin siyasar Alia.

Saboda haka, ya gargaɗi shugaban ƙasar da kada ya yi sakaci da ƙuri'un al'ummar Benue ta hanyar barin rikicin APC ya ci gaba ba tare da an magance shi ba.

Orbunde ya ce babban abin da ke barazana ga nasarar APC a jihar ba wai farin jinin Alia ko akasin haka ba ne, illa rarrabuwar kai, rashin amincewa da juna da kuma zargin rashin bin umarnin shugabancin jam’iyyar.

An gargadi Tinubu kan rikicin APC a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yayin zaman majalisar zartarwa. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Shawarar da dan siyasar ya bayar

Ɗan siyasar ya ce bai kamata shugaban ƙasa ya ci gaba da ƙyale rikice-rikicen cikin gida, takaddama kan shugabancin jam’iyya da rashin bin hukuncin kotu su raunana APC ba.

Kara karanta wannan

Atiku ya sake kifar da Tinubu, ya faɗi yadda zai dawo da tallafi, rage farashin fetur

Ya bayyana George Akume a matsayin sahihin jagoran siyasar Arewa ta Tsakiya, yana mai cewa tsohon gwamnan na daga cikin amintattun mutanen Tinubu kuma gogaggen ɗan siyasa.

A cewarsa, Akume ya kasance tare da Tinubu tun lokacin jam’iyyun Alliance for Democracy (AD) da Action Congress of Nigeria (ACN), har zuwa APC, cewar Punch.

Orbunde ya ce:

“Sakataren gwamnatin tarayya ya kasance amintaccen abokin tafiyar shugaban ƙasa tun daga AC, ACN har zuwa APC. Babu shakka kan amincinsa, amintakarsa da ƙwarewarsa wajen kawo nasara. Don haka, ya kamata shugaban ƙasa ya guji barin abin da yake da tabbas ya koma cikin wani yanayi marar tabbas.”

Akume ya fadi manyan makiyan Arewa

An ji cewa Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya ce duk ɗan Arewa mai neman shugabancin ƙasa a 2027 yana adawa da muradun yankin.

Akume ya ce an cimma yarjejeniyar karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu a Kaduna domin kiyaye haɗin kan Najeriya.

Ya yi kira ga ’yan Arewa da su goyi bayan Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, su jira har zuwa 2031 kafin neman shugabancin ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.