Atiku zai lallasa Buhari 60-40 a Katsina – Buba Galadima

Atiku zai lallasa Buhari 60-40 a Katsina – Buba Galadima

- Tsohon jigon jam'iyyar APC, Buba Galadima ya bayyana cewa dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar zai lallasa Shugaban kasa Buhari da kaso 60 zuwa 40 a arewa

- Galadima yace a mahaifar Buhari ta jihar Katsina kuwa sai dai suyi kunnen doki da Atiku

- Kakakin kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa na PDP ya kuma yi zargin cewa shugaba Buhari ya ki sanya hannu a dokar zabe saboda yana tsoron shan kashi

Buba Galadima, kakakin kungiyar kamfen din dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya bayyana cewa dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar zai lallasa Shugaban kasa Buhari da kaso 60 zuwa 40 a arewa.

Galadima ya bayyana cewa Atiku zai yi raba daidan kuri’u da Buhari harma a mahaifar Shugaban kasa, wato jihar Katsina.

Atiku zai lallasa Buhari 60-40 a Katsina – Buba Galadima

Atiku zai lallasa Buhari 60-40 a Katsina – Buba Galadima
Source: UGC

Galadima ya bayyana hakan a lokacin da ya bayyana a wani shirin gidan talbijin din Channels, na Politics Today a ranar Lahadi, 3 ga watan Fabrairu.

A cewarsa: “Atiku zai kayar da Buhari da kaso 60 zuwa 45. A wajen da za su yi 50-50 jihar Katsina ce.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta yanke wa masu laifi 40 hukunci cikin wata daya kacal

“A kudu maso yamma, zan fada ba shakku cewa mutanen Yarbawa na mutunta shugabanninsu, ba za su yi zabe na bangaranci ba.

Yace shugaba Buhari ya ki sanya hannu a dokar zabe saboda yana tsoron shan kashi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel