'Yan Bindiga Sun Tarfa Mutanen Gari da Daddare, Sun Kashe Mata, Yara da Matasa da Dama

'Yan Bindiga Sun Tarfa Mutanen Gari da Daddare, Sun Kashe Mata, Yara da Matasa da Dama

  • Akalla mutane 16, ciki har da mata, matasa da yara, sun mutu bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari kauyen Tafi Gana a jihar Filato
  • Mutane huɗu sun jikkata a harin da aka kai da misalin ƙarfe 11:30 na daren Laraba, 25 ga Nuwamba, 2026
  • Ƙungiyar Irigwe ta yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankulansu, kada su ɗauki doka a hannunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Plateau, Nigeria - Akalla mutane 16 ne suka rasa rayukansu bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari Tafi Gana, wani ƙaramin ƙauye da ke yankin Kyie Ihwien, kusa da Jebbu Miango a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.

Ƙungiyar Irigwe Development Association (IDA) ta bayyana cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na daren Laraba, 25 ga watan Nuwamba, 2026.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: An kashe mutane 5 suna cikin barci da tsakar dare a jihar Jigawa

Caleb.
Gwamnan jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang yana jawabi a wurin taro Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito vewa mutane huɗu sun kuma samu raunuka daban-daban, yayin da lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin ruɗani da fargaba.

Yadda ’yan bindigar suka kai harin

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiya, Sam Jugo, ya sanya wa hannu, wadda aka rabawa manema labarai a Jos, IDA ta ce maharan na ɗauke da bindigogin yaƙi da wasu muggan makamai.

Jugo ya bayyana cewa maharan sun shiga kauyen, sannan suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi.

“Sun kutsa cikin garin suka fara harbi ba kakkautawa, zuwa wayewar garin Alhamis, 26 ga Nuwamba, 2026, an gano gawarwakin mutane kusan 16, yayin da aka garzaya da wasu mutum huɗu da suka tsira zuwa wasu wuraren jinya da ba a bayyana ba."

Sunayen waɗanda suka mutu

Ƙungiyar ta fitar da sunayen mutanen da suka mutu a harin kamar haka:

  1. Moses Oko, mai shekara 70
  2. Maingwa Zere Rangya, mai shekara 60
  3. Danladi Ishaku, mai shekara 45
  4. Luka Danladi, mai shekara 21
  5. Elisha Luka, mai shekara 18
  6. David Danladi, mai shekara 10
  7. Ishaya Goslow, mai shekara 18
  8. Lami Danladi, mai shekara 30
  9. Isi Ishaku, mai shekara 18
  10. Zhime Ngaza, mai shekara 75
  11. ThankGod Danladi, mai shekara 18
  12. Gideon Joseph, mai shekara 25
  13. Ladi Abba, mai shekara 65
  14. Ruth Istifanus, mai shekara 20
  15. Mary Keyi, mai shekara 18
  16. Lazarus Musa, mai shekara 13

Kara karanta wannan

Gwamnatin Neja ta tabbatar da kashe mutum kusan 100 a jihar

Sanarwar ta ambato basaraken yankin, Nggwe Gado Dama, yana tabbatar da faruwar harin, tare da bayyana cewa an kai rahoton lamarin ga hukumomin tsaro, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Ƙungiyar Irigwe ta yi kira ga jama’a

Ƙungiyar IDA ta yi Allah wadai da kisan mutanen, tare da kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankulansu, su guji ɗaukar doka a hannunsu.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar Operation Enduring Peace, Kyaftin Polycarp Oteh, bai amsa tambayoyin yan jarida game da harin ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Yan bindiga sun kashe makiyaya 4

Kun ji cewa yan bindiga sun kashe aƙalla makiyaya huɗu, sannan suka yi awon gaba da shanu sama da 100 bayan kai hari a Ƙaramar Hukumar Qua’an Pan ta Jihar Filato.

Ƙungiyar MACBAN ta nuna damuwa kan harin, ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro su tabbatar da adalci da kariya ga kowa ba tare da nuna bambancin ƙabila ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262