Yanzu Yanzu: INEC ta kara ranakun karban katin zabe

Yanzu Yanzu: INEC ta kara ranakun karban katin zabe

Kasa da makonni biyu kafin zaben ranar 16 ga watan Fabrairu, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), ta tsawaita ranar karban katunan zabe na karshe zuwa Litinin, 11 ga watan Fabrairun 2019.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Takubu ya sanar da hakan a ranar Juma’a, 8 ga watan Fabrairu a lokacin wani ganawa da kwamishinonin zabe.

An yanke shawarar kara wa’adin ne bayan kwamishinonin zabe sun bayar da rahoto akan karban katunan zaben a jihohinsu daban-daban.

Da farko, Legit.ng ta rahoto cewa akwai yiwuwar kara wa’adin karban katunan zabe kamar yadda hukumar INEC ta bayyana.

KU KARANTA KUMA: Matasa 1,515 ke takarar kujerar majalisar dattawa da na wakilai

A baya mun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta tabbatar ma yan Najeriya cewa za ta gudanar da zaben gama gari na 2019 kamar yadda ta shirya, don haka ba za ta dage zaben kamar yadda wasu yan siyasa ke kiraye kiraye ba.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki a harkar zabe a ofishinsa dake babban birnin tarayya Abuja, inda yace duk da shari’un dake gaban kotu akan zaben fidda gwani na jam’iyyu, INEC ba zata dage zabenba.

Legit.ng ta ruwaito Farfesa Mahmood ya dauki alkawarin ba zai saba ma umarnin kotu ba, kuma ba zai ji shayin sauke nauyin daya rataya a wuyansa ba. “Kararrakin dake gaban kotu wanda suka samo asali dage zaben fidda gwanin jam’iyyun siyasa sun kai guda 640."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel