Nafiu Bala Ya Aika wa Atiku Abubakar Sakon Taya Shi Murnar Cika Shekara 80 a Duniya
- Nafiu Bala Gombe ya shiga sahun mutanen da suka taya Atiku Abubakar murnar cika shekaru 80 da haihuwa
- Tsohon mataimakin shugaban ADC na kasa ya yabi ‘dan adawar, ya ce rayuwarsa abin koyi ce ga matasa
- A jawabin da Nafiu Bala ya fitar a madadin shugabannin ADC, ya bukaci Atiku ya yi rajista da jam’iyyarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Nafiu Bala Gombe ya taya Atiku Abubakar murnar cika shekara 80 da haihuwa ganin zagayowar ranar 25 ga watan Nuwamba.
Matashin da ake rigimar shugabanci da shi a jam’iyyar ADC ya manta da sabanin nan, ya yi wa Atiku Abubakar fatan alheri a rayuwar shi.

Source: Facebook
Nafiu Bala ya taya Atiku Abubakar murna
Nafiu Bala ya fitar da jawabi mai taken ‘Sakon taya murna ga Alhaji Atiku Abubakar da ya cika 80’ a Facebook a ranar Laraba cikin dare.
Tsohon mataimakin shugaban na ADC ya ce ya fitar da jawabin ne a madadin shugabannin jam’iyyar ADC na kasa da ya ce suna karkashin sa.
Da yake yaba masa ganin ya cika shekara 80 da haihuwa, Nafiu Bala ya ce Wazirin Adamawa dattijo ne, mai kishin damukaradiyya kuma jagora.
Nafiu Bala ya bayyana rayuwar Atiku Abubakar a matsayin abin koyi ga dinbin matasan Najeriya.
A madadin halastaccen jagorancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin jagorancina, ina miƙa saƙon taya murna ta musamman ga mai girma tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, bisa murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta cika shekaru 80.
Muna taya fitaccen ɗan siyasa murna, wanda ya daɗe yana yi wa ƙasarmu hidima, kuma jajirtaccen mai kishin dimokuraɗiyya, wanda irin gudummawar da ya bayar na tsawon shekaru yake ci gaba da zama abin koyi ga matasan Najeriya.
- Nafiu Bala
Addu'ar da Nafiu Bala ya yi wa Atiku
Bayan ya jinjina, ‘dan siyasar ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki ya kara yi wa rayuwar Alhaji Atiku albarka kuma ya kare shi da lafiya.
"Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya albarkaci wannan sabon shekarunsa, Ya ba shi lafiya, tsawon rai, hikima da wadata, sannan Ya ƙara masa ƙarfi domin ci gaba da yi wa al’umma hidima."
- Nafiu Bala
Duk da sabaninsu, matashin ya yarda cewa an yi shekara da shekaru ana bugawa da Atiku a siyasa.
A lokacin da Atiku yake farin ciki da rana irin ta Laraba, Nafiu Bala ya jinginar da bambancinsu, lamarin da ya jawo martani iri-iri a kafar Facebook.
Har yanzu bai yi wa Atiku kallon 'dan APC
Ya yi amfani da jawabin wajen kira ga Atiku da ya zo a hada-kai da shi, ya yi cikakkiyar rajista da jam’iyyar ADC domin a ceto damukaradiyya.
Duk abin da ake yi, bangaren su Nafiu Bala suna ganin mutanen David Mark da kotun tarayya ta tsige su ba cikakkun ‘ya ‘yan jam’iyyar ADC ba ne.
Nafiu Bala ya ce:
"Yayin da muke taya shi murnar wannan gagarumin mataki a rayuwarsa, muna sake miƙa masa hannun zumunci, tare da sabunta kirarmu ta gaskiya gare shi da ya zo ya kasance cikakken ɗan jam’iyyar ADC, domin mu haɗa hannu wajen ceto dimokuraɗiyyarmu da gina Najeriya mai wadata.
"Barka da cika shekaru 80 da haihuwa, ran ka ya dade.
"Muna yi muku fatan ƙarin shekaru masu albarka, cikin ƙoshin lafiya da farin ciki."
Nafiu Bala zai fara yin kamfe a ADC
An ji labari cewa watakila Atiku Abubakar ya dace da mukami idan Nafiu Bala ya fara yakin neman zaben shugaban kasa mako mai zuwa.
Matashin ya nuna za su duba yiwuwar dauko Atiku Abubakar ya zama Darekta Janar na yakin neman zaben Farfesa Chris Uba a jam'iyyar ADC.
Hon. Nafiu Bala ya yi wannan magana ne lokacin da tsohon mataimakin shugaban Najeriyan yake ganin shi zai yi wa ADC takara a zaben 2027.
Asali: Legit.ng


