Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Shugaban kungiyar Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bukaci al’umman Najeriya da su duba Mutum mai gaskiya da rikon amana su zabe shi a matsayin Shugaban Kasa, a babban zaben da za a gudanar a watan gobe.
Ummi Zeezee ta koka ne cewa Atiku Abubakar ya aiko wa magoya bayan sa da ke farfajiyar finafinan Hausa da kudade masu yawa inda suka ware kan su sannan suka raba kudin ba tare da sun aika mata da kaso mai tsoka ba.
Uwargidar tsohon mataimakin Shugaban kasa, Amina Namadi-Sambo ta koka kan yadda akee tozarta matan Musulmi da ke sanya hiabi a wasu yankunan kasar, cewa hakan ya take hakkin yancin mata na yi kowace irin addini.
Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa Jirgin farko ya sauka a sabon tashar jirgin ruwa na Baro da ke Jihar Niger. A ranar Asabar 19 ga watan Janairu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da fara aikin tashar.
Wata kotun Majistare ta Osogbo, ta bada umarnin ci gaba da tsare wani matashi mai shekaru 23, da aka ambata da suna Peyemi Adeleke, akan zargin sa da ake yi da satar dan kamfai na mata. Adeleke ya musanta zargin da ake yi masa.
An kama wasu mutane uku a jiya a Yaba, jihar Lagas yayinda suke kokarin diban wasu jama’a a matsayin ma’aikatan wucin gadi na hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na bogi. Rundunar yan sandan jihar Lagas ta tabbatar da hakan.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Laraba, 23 ga watan Janairu a Sokoto ya sake jadadda alwashin da ya dauka na kin satar daga baitul malin kasar da kuma hana sauran mutane aikata hakan, ya ce zai ci gaba a kan haka.
Kungiyoyin mata daga kabilu daban-daban a kasar wadanda ke da zama a jihar Ebonyi sun marawa Atiku Abubakar baya. Sun zargi gwamnatin tarayya karkashin APC da gaza cika alkawaran zaben da ta daukar ma yan Najeriya.
Wata shaida ta bayyana cewa Maryam Sanda, wacce ake zargi da kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ta fada ma yan sanda cewa rikici da ya kaure tsakaninta da mijinta ya faru ne sanadiyar wasu hotunan tsaraicin wata mata a wayarsa.
Aisha Musa
Samu kari