Zolaya Buhari ke yi cewa da yayi kowa ya cika cikin sa in ma fitinan ne aje ayi – Kwamitin Kamfen

Zolaya Buhari ke yi cewa da yayi kowa ya cika cikin sa in ma fitinan ne aje ayi – Kwamitin Kamfen

Kungiyar kamfen din dan takrar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa ba daidai bane yadda ake ta yada jita-jitan wai Shugaban kasar ya yi kira ga mutanen Zamfara da su kwana da shirin ko ta kwana.

Daraktan labaran kungiyar, Festus Keyamo ya bayyana furucin shugaban kasar a matsayin barkwanci wanda aka san shugaban kasar dashi.

A ziyarar Kamfen da ya kai garin Gusau, Buhari ya ce ‘Ina son kowa ya cika cikin sa in ma fitinan ne aje ayi’.

Hakan bai yi wa mutane da dama dadi ba musamman ‘yan adawa inda suka rika cewa wannan magana bai dace ya fito daga bakin shugaban kasa ba.

Zolaya Buhari ke yi cewa da yayi kowa ya cika cikin sa in ma fitinan ne aje ayi – Kwamitin Kamfen

Zolaya Buhari ke yi cewa da yayi kowa ya cika cikin sa in ma fitinan ne aje ayi – Kwamitin Kamfen
Source: Facebook

Keyamo ya ce duka wanda ya san Buhari ya san si mutum ne mai yawan raha da barkwanci saboda haka ko a wancan lokacin da yake wannan bayani ya hada ne da zolaya ba wai da gaske yake yi ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Rikici ya barke a gangamin PDP a Lagas inda yan daba ke ta jifan junansu da kujeru

Sarakunan gargajiya na jihar Bayelsa sunyi jinjina ga shugaban kasa Muhammad Buhari bisa yaki da cin hanci da rashawa da yayi a kasar nan.

Sarakunan sun bayyana hakan ne a sakateriyar su dake Yenagoa a lokacin da suke karbar bakuncin Buhari. Shugaban kasar ya kai ziyara jihar ne dan yada manufar sa na kara tsayawa takara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel