Kwamishinan Ganduje Ya Kalubalanci Malamai kan Lamarin Sarkin Daura
- Tsohon kwamishinan harkokin addini a Kano, Dr. Tahir Baba Impossible, ya soki Sarkin Daura kan zargin da ake masa
- Baba Impossible ya bayyana cewa bai dace basarake mai daraja da martabar sarauta irin ta Sarkin Daura ya aikata hakan ba
- Malamin ya kuma yi kira ga malamai da su daina kare duk wanda ya aikata laifi, yana mai cewa babu bambanci tsakanin babba da ƙarami
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Tsohon kwamishinan addini a Kano, Dr. Tahir Baba Impossible ya tsoma baki kan zargin Sarkin Daura da ake yi.
Baba Impossible ya nuna damuwa kan yadda basaraken ya manta da girman da ke tare da shi na sarauta lokacin da aikata hakan.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani bidiyo da shafin AMC Hausa ya wallafa a shafin Facebook inda tsohon kwamishinan ya ba da shawarwari.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: An kai wa fitacciyar 'yar TikTok kuma 'yar Kwankwasiyya hari a Kano
Tsohon kwamishina ya magantu kan Sarkin Daura
Baba Impossible ya nanata cewa bai kamata basarake mai daraja kamar Sarkin Daura ya manta tasirin ragamar mulkinsa ya kusanci wata mata ba.
Ya soki wasu malamai da ke cewa bai kamata ana yayata bidiyon ba inda suke cewa ya kamata a rufa masa asiri.
Ya ce:
"Mutum mai sarauta irinsa, bai kamata yana taba hannun wata ba, a martabar sarauta da girma ba daidai ba ne, ko ba a zo shari'a ba.
"Na ji wasu malamai suna cewa a daina maganar, ba za a daina domin ta faru, yanzu kenan idan wani ne wanda bai isa ba, shi sai a yi maganarsa.
"Har na ji wani malami yana cewa Annabi ya ce ku girmama manyanu amma bai ce idan sun yi laifi ka da a fada ba."

Source: UGC
Shawarar da aka ba malaman Musulunci
Tsohon kwamishinan ya ce babu maganar mutum babba ne ko karami a Musulunci saboda addini ne na adalci.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, El Rufai ya tsage gaskiya a gaban kotu kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu
Ya shawarci malamai da su ji tsoron Allah yayin da suke karantarwa saboda Ubangiji ne ya ba su dama su fadakar da mutane.
"Babu zancen wani babba ko karami, a Musulunci ne ya ke basarake ko sarautar gargajiya yake, ko limamin masallaci aka kama shi yana lalata za a hukunta shi.
"Ku ji tsoron Allah malamai, Allah ya ba ku dama ne saboda abin da kuke dauke da shi, su kuma makafi ne ba gani suke yi ba, ba su iya fahimta sai abin da kuke fada masu, shiyasa mutane da yawa suka bata saboda sun yarda da ku."
- Baba Impossible
Sarkin Daura: An kafa kwamitin bincike
A wani labarin, an ji cewa Gwamna Dikko Radda ya kafa kwamiti na musamman domin gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa Sarkin Daura, Alhaji (Dr.) Umar Farouk Umar.
Gwamna Dikko Radda ya amince da kafa kwamitin, wanda zai binciki zargin tare da gano hakikanin abin da ya faru a fadar Sarkin a kwanakin baya.
Rahoto ya nuna cewa kwamitin zai gabatar da rahotonsa ga gwamnati cikin mako huɗu kan abin da ake zargin Sarkin a shi bayan rantsar da mambobinsa.
Asali: Legit.ng