Zaben 2019: Atiku, PDP na shirin shigo da makamai da kudade ta Kamaru - Nabena

Zaben 2019: Atiku, PDP na shirin shigo da makamai da kudade ta Kamaru - Nabena

- Jigon APC, Yekini Nabena ya zargi Alhaji Atiku Abubakar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da shirin hargitsa Najeriya

- Nabena yace Atiku da jam’iyyarsa na sirin fasa kaurin makamai da kudade daga Kamaru, ta iyakar Najeriya da Kamaru

- Kakakin APCn yace Atiku na da dangantaka mai karfi da kasar Kamaru

Mataimakin kakakin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Yekini Nabena ya zargi Alhaji Atiku Abubakar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da shirin hargitsa kasar gabannin zaben Shugaban kasa na 2019.

A cewar Nabena, Atiku da jam’iyyarsa na sirin fasa kaurin makamai da kudade daga Kamaru, ta iyakar Najeriya da Kamaru.

A cewar jigon n APC, an kulla makircin ne domin argitsa Najeriya a lokacin zaben kasa mai zuwa ta yadda za a jawo hankalin kasasen duniya don tausayi.

Mataimakin kakakin na APC yayi zargin ne a wani taron tattaunawa tare da manema labarai a Abuja a ranar Juma’a, 8 ga watan Fabrairu.

Zaben 2019: Atiku, PDP na shirin shigo da makamai da kudade ta Kamaru - Nabena

Zaben 2019: Atiku, PDP na shirin shigo da makamai da kudade ta Kamaru - Nabena
Source: Twitter

A baya mun ji cewa dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya koka kan zargin cewa ana kulla wani makirci don kama wasu daga cikin manyan hadimansa a harkokin zabe.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Babu wani hanya da za a rufe saboda ziyarar Buhari – Gwamnatin Lagas

Atiku ya zargi wasu gwamnoni da bai ambaci sunayensu ba daga arewa maso yamma da wani babban minista a wannan gwamnati da aiki tare da All Progressives Congress (APC), don cimma makircinsu.

Sai dai kuma kungiyar kamfen din Shugaban kasa Muhammadu Buhari tayi watsi da rade-radin sannan tayi gargadin cewa adawa ba wani lasisi na aikata laifi bane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel