Abin Tausayi: Yan Bindiga Sun Banka Wa Gari Wuta, Sun Ƙona Mutane da Ransu
- ’Yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Duhuwaya da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara, inda suka kashe wasu mazauna yankin
- Wata mazauniyar yankin ta ce an ƙona wasu tsofaffin mata masu shekaru tsakanin 70 zuwa 80 a raye
- Haka kuma, maharan sun tare hanyar Daki-Takwas Danzaure, suka harbi motoci biyu, suka yi garkuwa da wasu fasinjoji da direbobi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Wasu ’yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Duhuwaya da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara, inda suka ƙona gidajen kauyenntare da kashe mutane da dama.
Rahotanni sun ce harin ya faru ne da yammacin Lahadi, lamarin da ya jefa al’ummar ƙauyen cikin jimami tare da tilasta wa wasu barin gidajensu.

Source: Original
Wata mazauniyar yankin mai suna Hadiza Namdas ta shaida wa jaridar Leadership cewa maharan sun ƙona gidaje da dama, ciki har da waɗanda wasu tsofaffin mata masu shekaru tsakanin 70 zuwa 80 ke zaune a ciki.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Mutane da dama sun mutu da aka yi yunkurin kashe sanata a wurin kamfe
An ce maharan sun kona tsofaffin matan a raye. An kuma ruwaito cewa maharan sun harbe wasu matasa biyu har lahira yayin harin.
Mahara sun tare hanyar Daki-Takwas
Tun da farko a wannan rana, da misalin ƙarfe 11:00 na safe, ’yan bindigar sun tare hanyar Daki-Takwas Danzaure na kusan awanni biyu.
Wani mai sana’ar achaba, Yusuf Sahabi, ya ce maharan sun harbi motoci biyu, suka yi garkuwa da wasu fasinjoji da direbobi, sannan suka harbi wani mai babur wanda ya tsallake rijiya da baya kafin maharan su kwace babur ɗinsa.
Wannan hari ya ƙara jefa tsaro a yankunan karkara na Jihar Zamfara cikin damuwa, inda mazauna yankunan ke ci gaba da fuskantar hare-hare, kashe-kashe, raba mutane da muhallansu da kuma lalata dukiyoyi.
A lokacin haɗa wannan rahoto, ana ci gaba da ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara da gwamnatin jihar kan lamarin.
Mazauna yankin sun yi kira ga hukumomin tsaro da gwamnatin jihar da su gaggauta ɗaukar mataki domin dawo da zaman lafiya a Bukkuyum da sauran yankunan jihar da ke fuskantar barazanar hare-hare.
Wasu bayanai sun nuna cewa kaiyen Duhuwaya ya zama kusan kufai sakamakon yadda yan bindiga suka kona gidaje, tre da tarwatsa mutane, wadanda suka bar gidajensu domin neman tsira.
Asali: Legit.ng