Tinubu Ya Nuna Damuwa kan Ɗalibai 78 da Aka Sace, Ya Ɗauki Alƙawari Mai Girma

Tinubu Ya Nuna Damuwa kan Ɗalibai 78 da Aka Sace, Ya Ɗauki Alƙawari Mai Girma

  • Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ceto ɗaliban da aka sace a jihar Borno.
  • Tinubu ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin siyasar APC a Maiduguri, inda ya kuma yaba wa jami’an tsaro bisa sadaukarwar da suke yi
  • Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya gode wa Tinubu kan ayyukan raya ƙasa da gwamnatin tarayya ta gudanar a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sha alwashi game da sace dalibai da aka yi a jihar Borno a Arewacin Najeriya.

Tinubu ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an kuɓutar da ɗaliban da wasu ’yan ta’addan Boko Haram suka yi garkuwa da su a jihar.

Kara karanta wannan

Atiku ya sake kifar da Tinubu, ya faɗi yadda zai dawo da tallafi, rage farashin fetur

Tinubu ya dauki alkawari a Borno
Gwamna Babagana Zulum da manyan APC yayin da Bola Tinubu ke jawabi a Borno. Hoto: All Progessives Congress.
Source: Facebook

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Maiduguri, yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar APC a wajen gangamin siyasar shiyyar Arewa maso Gabas da aka gudanar a filin wasa na El-Kanemi, cewar Punch.

Tinubu ya fadi aniyar gwamnatinsa

Shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar kuɓutar da ɗaliban da aka sace daga makarantar firamare ta Mussa da kuma makarantar sakandaren gwamnati ta Lassa, da ke ƙaramar hukumar Askira-Uba.

Rahotanni sun nuna cewa kimanin ɗalibai 78 ne aka yi garkuwa da su a waɗannan makarantu.

Tinubu ya ce:

“Za mu yi duk mai yiwuwa domin kuɓutar da ɗaliban da aka yi garkuwa da su a al’ummomin Mussa da Lassa.
“Addu’o’inmu, dakarun sojinmu da jami’an leƙen asirinmu na tare da su. Za mu kuɓutar da su, in Allah ya yarda.”
Tinubu ya sha alwashin kwato ɗalibai da aka sace
Taswirar jihar Borno da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Tinubu ya yabawa dakarun sojoji

Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa dakarun soji da sauran jami’an tsaro bisa sadaukarwar da suke yi, musamman waɗanda ke bakin daga wajen yaƙi da ta’addanci.

Kara karanta wannan

Barau Jibrin ya hada kan malaman Musulunci 2,000 saboda Tinubu, Abba Kabir

Ya tabbatar musu da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba su goyon baya domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin Arewa maso Gabas.

Tinubu ya ce gwamnati na girmama jami’an tsaron da ke gudanar da ayyukansu cikin daji, rana da ruwan sama, tare da sadaukar da rayukansu domin tabbatar da zaman lafiya a Maiduguri da sauran sassan Borno.

Ya kuma yi kira ga ’yan ta’adda da masu aikata fashi da makami da su ajiye makamansu tare da miƙa wuya ga hukumomin tsaro, yana mai cewa akwai damar sauya salon rayuwarsu.

Gwamna Zulum ya godewa Tinubu

A nasa jawabin, gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya gode wa Shugaba Tinubu bisa zaɓen Maiduguri a matsayin wurin gudanar da gangamin siyasar APC na shiyyar Arewa maso Gabas.

Zulum ya bayyana jin daɗinsa kan yadda magoya bayan APC suka fito da dama tare da gudanar da taron cikin lumana da tsari, cewar Vanguard.

Gwamnan ya ce jihar Borno ta amfana sosai da shirin Renewed Hope Agenda na gwamnatin tarayya, inda ya ambaci wasu manyan ayyukan raya ƙasa da suka haɗa da hanyar Gombe zuwa Biu zuwa Maiduguri.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya samu matsala yana aske gemu a fadar shugaban kasa

Tinubu ya taya Atiku murna

An ji cewa shugaba Bola Tinubu ya taya tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, murnar cika shekaru 80 da haihuwa.

Tinubu ya bayyana cewa ya goyi bayan takarar Atiku ta shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Action Congress, duk da bambance-bambancen siyasa.

Shugaban ya yabawa Atiku kan gudunmawarsa ga siyasar Najeriya, harkokin kasuwanci da ilimi, musamman kafa Jami'ar Amurka a Yola.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.