Zaben 2019: Tapgun ta sauya sheka daga PDP zuwa APC a Plateau

Zaben 2019: Tapgun ta sauya sheka daga PDP zuwa APC a Plateau

Tsohuwar ministar kasuwanci a karkashin gwamnatin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, Misi Josephine Tapgun ta sauya sheka daga jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC), jaridar Daily Sun ta ruwaito.

Da take Magana akan sauya shekar ta, Misis Tapgun tace ta koma APC ne domin ta marawa tazarcen Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Simon Lalong da yan takarar jam’iyyar baya a zabe mai zuwa.

A cewar rahoto, Tapgun ta sauya sheka ne a ranar Litinin, 4 ga watan Fabrairu a lokacin gangamin kamfen din dan takarar sanata na kudancin Plateau, a karamar hukumar Shendam da ke jihar.

Zaben 2019: Tapgun ta sauya sheka daga PDP zuwa APC a Plateau
Zaben 2019: Tapgun ta sauya sheka daga PDP zuwa APC a Plateau
Asali: Twitter

Ta bayyana cewa ta koma APC be sakamakon nasarorin da shugaba Buhari da Gwamna Lalong suka samu wajen yakar rashin tsaro, cin hanci da rashawa da kuma talauci.

Gwamna Simon Lalong yayi wa Tapgun barka da zuwa jam’iyyar sannan ya sha alwashin samar da sarari ga dukkanin mambobin jam’iyyar ba tare da nuna banbanci ba.

KU KARANTA KUMA: Mambobin SDP da PDP 2,000 sun sauya sheka tare da tsohon mataimakin gwamnan Ondo zuwa APC

A cewarsa, PDP ta bar jihar cikin yunwa, rashin tsaro da rashin biyan albashi hade kuma da rikicin addini inda yace APC ta magance dukkanin rikice-rikice kuma ba za a taba komawa baya ba.

Ya bayyana cewa shugaba Buhari na dauke da mutanen Plateau a zukiya sannan yana aiki domin farfado da mutanen jihar da suka wahala saboda rashin tsaro.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel