Bayan Kamfe Ya Kankama, An Sake Neman Atiku Ya Janye daga Takarar Shugaban Kasa a 2027
- Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Bode George, ya bukaci Atiku Abubakar ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027
- George ya ce ya kamata Atiku ya jira har zuwa 2031, lokacin da ya ce kujerar shugaban ƙasa za ta koma Arewa
- Jigon PDP ya kuma nuna damuwa kan sabanin hukuncin kotuna da kuma tasirinsu ga zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Bode George, ya yi kira ga ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Alhaji Atiku Abubakar, da ya janye daga takarar zaɓen 2027.
George ya ce bisa tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu, ana sa ran kujerar shugaban ƙasa za ta koma Arewa a shekarar 2031, don haka Atiku zai iya sake neman takarar a lokacin.

Kara karanta wannan
Atiku ya taso Tinubu da NNPCL gaba a yi bayanin inda Naira tiriliyan 1.4 ya maƙale

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Bode George ya bayyana hakan ne yayin da yake Da yake magana da ’yan jarida ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamba, 2026.
George ya bayyana cewa burin Atiku na sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 ya saɓa wa fahimtar raba madafun iko tsakanin Arewa da Kudu da waɗanda suka kafa PDP suka amince da ita.
Ya ce an ƙirƙiro tsarin ne tun farkon Jamhuriya, sannan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alex Ekwueme, da sauran waɗanda suka kafa PDP suka ƙarfafa shi. A cewarsa, ya kamata a mutunta tsarin domin tabbatar da zaman lafiyar siyasa da adalci.
George ya shawarci Atiku ya jira
Da yake tambayar dalilin da ya sa Atiku ke ci gaba da neman shugabancin ƙasa, George ya ce ya kamata tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bar Kudu ta kammala nata wa’adin kafin ya sake neman kujerar.
Ya ce:

Kara karanta wannan
Atiku ya sake kifar da Tinubu, ya faɗi yadda zai dawo da tallafi, rage farashin fetur
“Shin Atiku ne kaɗai ɗan Arewa a Najeriya? Me ya sa yake neman wannan kujera duk bayan shekara huɗu? Me ya sa yake da tsananin burin mulki? Ya riga ya cika shekara 80. Ina son in ba shi shawarar ya manta da burinsa na zama shugaban ƙasa a shekara mai zuwa.
“Ya kamata ya dawo a 2031, lokacin da kujerar za ta koma Arewa. A lokacin zai kusan cika shekara 85, kuma ’yan Najeriya ne za su yanke shawarar ko suna son zaɓensa ko a’a.”
Ya soki sabanin hukuncin kotuna
A kan ƙarar da ake yi a kotuna tsakanin jam’iyyun siyasa gabanin zaɓe, George ya nuna damuwa kan abin da ya kira rashin daidaito a yadda ɓangaren shari’a ke shiga harkokin siyasa, cewar rahoton Vanguard.

Source: Facebook
Ya yi gargaɗin cewa hukuncin kotuna masu saɓani da cin karo da juna kan batutuwa iri ɗaya na iya haifar da rashin tabbas game da gudanar da babban zaɓen 2027.
Ya kuma tambayi ko har yanzu ana kallon ɓangaren shari’a a matsayin wurin share hawayen talaka, musamman ganin yadda ’yan siyasa ke ci gaba da fuskantar shari’o’i kan shugabancin jam’iyyu da zaɓen ’yan takara.
Atiku ya nanata alkawurransa
Kun ji cewa Atiku Abubakar ya yi alkawarin rage farashin man fetur, dawo da tallafin mai da kuma ƙarfafa darajar Naira idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC ya bayyana cewa zai inganta rayuwar ’yan Najeriya ta hanyar bunƙasa masana’antun cikin gida.
Asali: Legit.ng