Buhari ba mutum bane mai tsananin son mulki – Inji Oshiomhole

Buhari ba mutum bane mai tsananin son mulki – Inji Oshiomhole

Shugaban Jam’iyyar All Pregressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba mutum bane mai tsananin son mulki ta ko halin ka-ka

Oshiomhole ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 14 ga watan Fabrairu a wani taron manema labarai a birnin tarayya, Abuja, inda ya bayyana musu cancantar Buhari wanda ke neman shugabancin kasar a karo na biyu.

Ya ce Buhari na bukatar karin wasu shekaru hudu domin ya ci gaba da kokarin da ya fara na sake bunkasa Najeriya.

Buhari ba mutum bane mai tsananin son mulki – Inji Oshiomhole
Buhari ba mutum bane mai tsananin son mulki – Inji Oshiomhole
Asali: Facebook

Shugaban na APC yace tunda dai dokar kasa ta ba shi damar sake tsayawa takara, to ya cancanta a sake zaben sa domin shi ne zai iya kai Najeriya zuwa mataki na gaba.

KU KARANTA KUMA: Zabe: IG ya bayar da umurnin takaita zirga-zirgan ababen hawa

Oshiomhole ya jadadda cewa Buhari ba mutum bane da dole-dole sai ya ci gaba da zama a kujerar mulki ba. Ya yi alkawarin gudanar da sahihin zabe. Kuma idan ya yi nasara, to zai kara kai kasar nan matakin nasarar kayan more rayuka da inganta tattalin arziki.

Daga nan sai ya ce idan an je zabe ranar Asabar, to a zabi APC, kuma a tuna abubuwan da dan takarar ahugaban kasa a karkashin PDP, Atiku Abubakar ya rika furtawa a wurin kamfen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Kn samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel