Shugaba Buhari ya cancanci yabo – Inji dan Sule Lamido

Shugaba Buhari ya cancanci yabo – Inji dan Sule Lamido

Dan takarar kujerar Sanatan Jigawa ta Tsakiya a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Mustafa Sule Lamido, ya bayyana cewa ya samu karin karfin guiwar fitowa takara sakamakon amincewa da dokar ba matasadamar yin takara wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba ma hannu.

Mustafa wanda da ne ga tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin PDP, ya yi wannan jawabi ne a ranar Alhamis, 31 ga watan Janairu a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.

Ya ce shigo da dokar ya yi fa’ida domin da a ce ba a shigo da dokar ba, to da bai samu kwarin guiwar fitowa takarar ta sanata ba.

Shugaba Buhari ya cancanci yabo – Inji dan Sule Lamido
Shugaba Buhari ya cancanci yabo – Inji dan Sule Lamido
Asali: Twitter

Ya jinjina wa Majalisar Tarayya saboda shigo da dokar da kuma goya mata baya da suka yi.

Mustafa ya ce ya na da yakinin samun nasara, saboda abin da ya kira rashin kyakkyawan wakilci da sanatan APC da ke kai, Sabo Nakudu ke yi wa shiyyar mazabar sa.

KU KARANTA KUMA: Yarinya yar shekara 9 ta nitse cikin rijiya a jihar Jigawa

A baya mun ji cewa Gwamna Nasir El-Rufai yayi martani akan kin sanya hannu a dokar gyaran zabe da Shugaba Buhari ya ki yi. El-Rufai yace da Shugaban kasar ya sani ya sanya hannu akan dokar zaben

Gwamnan yace a nazarin da yayi babu wani takamaimen abin da ya sauya sabon kudirin dokar daga Dokar Zabe ta ainihi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel