Mambobin PDP sun koma APC a Akwa Ibom

Mambobin PDP sun koma APC a Akwa Ibom

- Mambobin jam’iyyar APC da dama a jihar Akwa Ibom sun koma jam’iyyar APC

- Sun zargi Gwamna Emmanuel da rashin kula da jin dadin wadanda ke aiki a kasarsa

- Daga cikin masu sauya shekar harda tibe Ibanga, wani hadimin Gwamna Udom Emmnuel

Mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dama a jihar Akwa Ibom sun koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Daya daga cikin masu sauya shekar shine tibe Ibanga, wani hadimin Gwamna Udom Emmnuel. Ibanga ya kasance hadimin Gwamna Emmanuel kan ayyuka

Sauran masu sauya shekar sun hadada tsohon Shugaban karamar Ikot Ekpene David Umana. Masu sauya shekar sun koma APC ne a lokacin gangamin kamfen a babban filin wasa na Ikot Ekpene.

Mambobin PDP sun koma APC a Akwa Ibom
Mambobin PDP sun koma APC a Akwa Ibom
Asali: UGC

Ibanga yace ya bar gwamnatin ne saboda gwamnan bai kula da jin dadin hadimansa.

Emmanuel ya fuslanci yawan murabus daga gwamnatinsa a yan kwanakin nan inda hadimansa ke ta barinsa, inda suka kafa hujja da rashin samun kula daga gwamnan.

Wadanda suka yi murabus daga matsayinsu sun hada da: Chris Okorie (hadimi na musamman kan lamuran zabe); Elder Ibanga Etang (hadimi na musamman kan kula da ayyuka); Fasto Abasiandikan Nkono (hadimi na musamman kan ayyuka) Utibe Idem (hadimi na musamman kan ayyuka); Umo Assiak (hadimi na musamman kan ayyuka) da kuma Anietie Ebe (hadima na musamman kan kula da ayyuka).

KU KARANTA KUMA: Goyon bayan Atiku babu abunda zai canja a sakamakon zaben Shugaban kasa – Kungiyar Arewa

Sauran sune: Mfon Udeme (hadimi na musamman kan lamuran zabe); Joe Iniodu (hadimi na musamman kan harkokin labarai); Idorenyin Esikot (hadimi na musamman kan kananan ciniki); Dr. Anthony Usoro (babban hadimi kan tsar-tsare); Godswill Ekpenyong (hadimi na musamman kan ayyuka) da kuma Derek Tower Umoh (hadimi na musamman kan ayyuka).

Kwamishinoni biyu; Victor Antai da Ibanga Akpabio ma sun yi murabus sun bar PDP zuwa APC.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel