Ba za mu taba daga zabe ba duk da kalubalen da muke fuskanta – INEC

Ba za mu taba daga zabe ba duk da kalubalen da muke fuskanta – INEC

- Hukumar zabe mai zaman kanta tace duk rintsi duk wuya bata ga dalilin da zai sanya ta daga zaben kasar ba

- INEC tace duk da tarin kalubale da take fuskanta a yanzu toh babu makawa za ta gudanar da zaben kasar

- A ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu ne za a gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar dokokin kasa

Duk da tashin gobara da ya afku a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta har uku, a ranar Laraba, 13 ga watan Fabrairu, hukumar tace ba za ta dage zaben kasar da aka shirya gudanarwa a ranar 16 ga watan Fabrairu ba.

Shugaban hukumar, Mahmood Yakubu yace koda dai gobarar ya kawo tsakiko a shirye-shiryen da INEC ke yi don yin zabe cikin lumana, hukumar za ta gudanar da zabenta.

Ba za mu taba daga zabe ba duk da kalubalen da muke fuskanta – INEC

Ba za mu taba daga zabe ba duk da kalubalen da muke fuskanta – INEC
Source: UGC

Yakubu ya yi jawabin ne ta hannun daya daga cikin kwamishinoninta, Festus Okoye, cewa babu wani dalili da zai sanya hukumar daga zaben da ta shirya gudanarwa a ranar da tayi niya.

KU KARANTA KUMA: Dubban mutane sun yi tururuwan fitowa domin tarban Buhari a Katsina

A halin da ake ciki, mun samu labari jiya cewa hukumar zabe na kasa watau INEC, ta bayyana cewa maganar da ake ta yadawa na cewa an canza yatsar da ake amfani da shi wajen dangwala kuri’a a zaben da za ayi kwanan nan sam ba gaskiya bane.

Hukumar zabe mai zaman kan-ta na INEC, tace masu kada kuri’a za su iya amfani da kowane yatsa su ka ga dama wajen dangwalawa zabin su. INEC tace babu ruwan takardun ta da yatsar da aka yi amfani da shi wajen kada kuri’a.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel