Yanzu Yanzu: Jami’an hukumar INEC za su sake zama

Yanzu Yanzu: Jami’an hukumar INEC za su sake zama

Bayan korafe-korafe daga jam’iyyan Peoples Democratic Party (PDP) da All Progressives Congress (APC) suka yiwa hukumar zabe na kasa akan dage zabe har na tsawon sati daya da tayi, hukumar zata yi zama yau don sake duba lamarin.

A cewar Sakataren yada labarai na shugaban hukumar INEC ta kasa, Mista Rotimi Oyekanmi, hukumar zata yi zama don sake duba matsayinta da kuma shawararta na cigaba ko kada a cigaba da yakin neman zabe.

Jam’iyyun guda biyu sun yi korafin cewa hani da hukuman tayi bata da fa’ida a doka.

Yanzu Yanzu: Jami’an hukumar INEC za su sake zama

Yanzu Yanzu: Jami’an hukumar INEC za su sake zama
Source: Original

Jam’yyan PDP tayi zargin cewa akwai hujjoji wadanda ke tabbatar da cewa ma’aikatu Gwamnatin Tarayya tare da jam’iyyar APC suna shirin yiwa hukumar INEC barna don shirya zaben shugaban kasa, Wanda hakan ya sabawa ra’ayin fadar shugaban kasa da shugaban jam’iyyan na kasa, Mista Adams Oshiomhole.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotun Kano ta bayar da belin Deji Adeyanju

Har ila yau Jam’iyyar adawa ta bukaci hukumar zabe da ta janye shawararta akan tsayar da yakin neman zabe na jam’iyyu, mataki wandaDarektan sadarwa na kungiyan yakin neman zaben shugaban kasa, Mista Festus Keyamo, SAN, ya bayyana cewa hana jam’iyyun siyasa gudanar da yakin neman zabe a matsayin abunda ya sabawa doka, duk da daga zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel