An Samu Bayanin Adadin Gwamnonin da Suke tare da Shugaba Tinubu a 2027

An Samu Bayanin Adadin Gwamnonin da Suke tare da Shugaba Tinubu a 2027

  • Gwamnan Imo ya ce gwamnonin APC na nan daram wajen goyon bayan Bola Tinubu duk da tulin furofaganda da yake sha
  • Hope Uzodimma ya sha alwashin cewa gwamnoninsa za su tallafa wa shugaban Najeriyan ta hanyar taimakonsa a jihohinsu
  • Sanata Uzodimma ya yaba wa Tinubu saboda irin shugabancinsa, yana ganin manufofinsa sun bunƙasa tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Imo - Gwamnan jihar Imo kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin APC ta PGF, Hope Uzodimma, ya sake jaddada goyon bayansu ga shugaban ƙasa.

Mai girma Hope Uzodimma ya ce duka gwamnonin APC 31 suna tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana cewa za su ci gaba da mara masa baya.

Bola Tinubu
Bikin kaddamar da littafin tarihin Bola Tinubu Hoto: Comr. Jeremy Banji
Source: Facebook

Gwamnonin APC na tare da Bola Tinubu

Leadership ta rahoto shi ya ce duk da furofaganda da sauran matsalolin da yake fahimta, shi da sauran takwarorinsa a APC suna tare da Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nuna damuwa kan ɗalibai 78 da aka sace, ya ɗauki alƙawari mai girma

Hope Uzodimma ya bayyana cewa gwamnonin sun amfana da shugabancin Tinubu, don haka za su nuna goyon bayansu ga gwamnatinsa a zaɓen 2027.

Ya shaida hakan ne a ranar Talata a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, yayin bikin ƙaddamar da littafin da fitaccen ɗan jarida, Sam Omatseye, ya rubuta.

Marubucin ya wallafa littafin tarihin mai suna From AD to APC: The Evolution of Nigerian Political Parties and the Exploits of One Man (1998–2015).

Gwamnan Imo wajen bikin kaddamar da littafin Tinubu

Gwamnan ya ce sun halarci taron ne domin girmama tarihin Tinubu da gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa tafiyar siyasar masu ra'ayin ci gaba a ƙasar.

Ya ce tarihin siyasar shugaban ƙasar abin koyi ne ga sababbin 'yan siyasa, yana mai cewa gwamnoninsu na jam’iyyar APC na nan daram tare da shi.

Uzodimma ya yaba wa Mista Omatseye bisa rubuta tarihin yadda Tinubu ya tashi daga AD zuwa APC, ya ce littafin zai taimaka wajen adana tarihin siyasa.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa ta ɓullo, ana zargin wasu mutane na yaudarar Tinubu gabanin zaben 2027

Ya kuma bukaci masana da masu bincike su ci gaba da tattara bayanai kan labarin siyasar Tinubu, domin a cewarsa, littafi guda ba zai iya ƙunsar komai ba.

Gwamnoni suna ci moriyar tsare-tsaren Tinubu

Gwamnan ya kuma danganta nasarar da gwamnatocin jihohi ke samu ta fuskar tattalin arziki da gina abubuwan more rayuwa da salon shugabancin Tinubu.

Dangane da zaɓen 2027 kuwa, Uzodimma ya ce gwamnonin da ke PGF sun ɗauki alhakin nuna goyon bayansu ga Tinubu ta hanyar tallata sa a jihohinsu.

An rahoto shi ya ce akwai alamun Tinubu na ƙara karbuwa a ƙasar, duk da cewa masu sukar gwamnatinsa da masu yaɗa farfaganda suna ta yi a yau.

A ƙarshe, gwamnan ya sake jaddada amanarsa da na sauran mambobin ƙungiyar gwamnonin APC ga Tinubu, ya ce suna tare da tazarcen shi a takarar 2027.

PGF za ta mara wa shugaba Tinubu baya wajen neman wa'adin mulki na biyu kuma yana da kwarin guiwar zai aiwatar da manufofinsa idan ya sake yin galaba.

Tinubu
Littafin Bola Tinubu da aka rubuta Hoto: Comr. Jeremy Banji
Source: Facebook

Dalilin Kashim Shettima na sukar Atiku Abubakar

Kashim Shettima yana girmama Atiku Abubakar a matsayin dattijo a siyasa, amma an ji ya ce ba zai daina caccakar shi ba kamar yadda aka samu labari.

Kara karanta wannan

Sanata ya yi nadamar goyon bayan gwamna har ya hau kujerar mulki, ya nemi afuwa

Mataimakin shugaban ƙasar yana sukar Atiku Abubakar ne saboda wasa da ke tsakanin Fulani da Kanuri.

Ya bayyana cewa Peter Obi, Rabiu Kwankwaso, Seyi Makinde da Rotimi Amaechi abokansa ne, kuma bai taɓa zaginsu ba duk da bambancin jam'iyyunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng