Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Gidauniyar Al-Thaqalayn wacce ta kasance bangare guda na kungiyar Shi’a ta bayyana kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) wacca Sheikh Ibraheem El-Zakzaky ke jagoranta a matsayin na jabu.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan ya sanar da kwamitocin majalisar dattawa, inda ya ambaci sunayen shugabanni da mataimakin shugabannin kwamitocin.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 30 ga watan Yuli, yace ba zai ambaci sunan wanda zai gaje shi ba a 2023. Buhari yayi magana ne yayinda ya karbi bakuncin mambobin kungiyar Progressives in Academics (Pro-Acad).
Yan bindiga a sun kai hari kauyuka hudu a karamar hukumar Batsari dake jihar Katsina a yammacin ranar Lahadi, inda suka kashe mutane uku sannan suka yi garkuwa da mutane shida.
Rahotanni sun kawo cewa a safiyar ranar Lahadi, 28 ga watan Yuli wasu yan bindiga, sun kashe wani fitaccen dan kasuwa a garin Gulma da ke jihar Kebbi, Alhaji Usuf Garkar-Bore sannan suka yi garkuwa da surukarsa, Aisha.
Idan aka ce Hepatitis, toh ana nufin ciwon Hanta kenan a Hausance. Hepatitis kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka hada da; Hepatitis A, Hepatitis B, Hepatitis C, Hepatitis D, Hepatitis E.
Ramatu ta kasance tana sana’ar sayar da charbin malam (alawar gargajiya), inda ta bayyana cewa tana samun naira miliyan daya da dubu dari hudu a kowani mako daa cikin wannan sana’a tata.
Alhaji Umaru Badami, mahaifin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa, ya rasu. Badami mai shekara 82, ya rasu ne a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuli, bayan yayi fama da rashin lafiya, Solomon Kumangar ya sanar da hakan.
Fitaccen jarumn Kannywood mai suna Tijjani Asase ya karyata rade-radin da ke yawo kan cewa barayin Babura sun kashe dansa mai suna Sadauki. Yace suna nan lafiya daga ciki har dansa, babu wani matsala daya faru dashi.
Aisha Musa
Samu kari