Ina samun naira miliyan daya da dubu dari hudu duk sati daga saida charbin malam – In ji wata yar Katsina
Lallai babu shakka idan Allah ya sanya wa sana’ar mutum albarka, sai ka ga ya daukaka fiye da tunanin mutane, hakan ce ta kasance ga wata yar kasuwa mai suna Ramatu daga jihar Katsina.
Matar ta kasance tana sana’ar sayar da charbin malam (alawar gargajiya), inda ta bayyana cewa tana samun naira miliyan daya da dubu dari hudu a kowani mako daa cikin wannan sana’a tata.
Ana daukar Ramatu wacce mazauniya kauyen Fadima a (Katsina) a matsayi na ma'aikaciya kuma itace mai mafi girman ma'aikatar aikinyi na hannu a cikin garin ta, ba tare da ilimin zamani ba, babban aikinta bayan zamanta Uwargida shine kasuwancin sana'ar alawar gargajiya wanda aka santa da shi.
Gidanta cike yake a kullun tare da maikata sama da 70 ciki har da matasa maza da mata, suna aikin kulla 'Charbin Malam'.
A wata hira da mujjalar Cliqq ta yi da ita game da adadin ribar da take samu a kullun daga wanda take sayarwa da -tallatawa, sai ta ce “A kullum ina samun N200,000 ”.
Ta bayyana cewa tana sayan buhuhunan sukari goma sha uku (13) a kullun akan kudi N13,500 na kowane jaka.
KU KARANTA KUMA: ‘Yan Majalisa sun kyauta da su ka tantance Akpabio a matsayin Minista - Sanata Folarin
Hakan yana nuna cewa Ramatu tana siyan jakunkuna sukari sama da guda 91 a duk sati domin gudanar da kasuwancinta yayin da take cin ribar kimanin Miliyan N1.4 a duk sati a siyar da alawar gargajiya wanda yanzu ake siyarwa a yankuna kananan hukumomi 34 na jihar Katsina, da kuma wasu gurare.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng