Hukumar INEC Ta Fara Dora Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Ekiti a Shafin IReV
- Hukumar INEC ta fara dora sakamakon zaben gwamnan jihar Ekiti a shafin tattara sakamako na IReV bayan jinkirin da aka samu
- Rahoto ya nuna cewa INEC ta fara ɗora sakamakon ne da misalin ƙarfe 4:10 na yammacin ranar Asabar
- Hakan na zuwa ne bayan kungiyar Yiaga Africa, mai sa ido a harkokin zabe, ta gano wasu matsaloli da aka samu a kyayyakin zaben Ekiti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ekiti, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta fara ɗora sakamakon rumfunan zaɓe na zaɓen gwamnan jihar Ekiti a shafinta na IReV fiye da sa’o’i biyu bayan kammala kaɗa ƙuri’a.
Hukumar ta fara ɗora sakamakon ne da misalin ƙarfe 4:10 na yammacin ranar Asabar bayan an fara nuna damuwa kan rashin ganin sakamakon a shafin tattara sakamako na INEC.

Source: Facebook
INEC ta fara dora sakamako a IReV
Jaridar The Cable ta rahoto cewa kafin a fara ɗora sakamakon, hotunan takardun sakamakon zabe daga rumfunan zaɓe sun riga sun fara yawo a kafafen sada zumunta.
Rahoton da aka fitar daga shafin ya nuna cewa an tura sakamakon rumfunan zaɓe 514 cikin 2445 inda aka gudanar da zaɓe a jihar Ekiti zuwa shafin IRev zuwa yanzu.
Wannan ya nuna kashi 21.02 cikin 100 na sakamakon zaɓen an ɗora su shafin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
An fara gano matsaloli a zaben Ekiti
Jinkirin ɗora sakamakon a sahfin IReV na INEC ya zo ne bayan kungiyar Yiaga Africa ta nuna damuwa kan wasu rashin daidaito da aka samu a kayan aikin zaɓen da aka tanada domin gudanar da zaɓen.
A cikin wata sanarwa da Aisha Abdullahi, shugabar tawagar sa ido ta Yiaga Africa, da daraktan ƙungiyar, Samson Itodo, suka fitar, sun ce akwai bambance-bambance a takardun zaɓe, fom ɗin sakamako da jerin sunayen ‘yan takarar da INEC ta wallafa.

Kara karanta wannan
Ekiti 2026: Rigima mai zafi ta kaure tsakanin magoya bayan APC da ADC bayan an jibge kudi
A cewarsu, fom ɗin sakamakon rumfar zaɓe EC8A ya tanadi wuraren jam’iyyu 15, yayin da takardun zaɓe ke ɗauke da jam’iyyu 19, amma jerin sunayen ‘yan takarar da INEC ta sabunta a ranar 18 ga Yuni, 2026 ya nuna jam’iyyu 14 ne suka gabatar da ‘yan takara.

Source: Facebook
Yiaga ta nemi karin bayani
Yiaga Africa ta bayyana cewa hukuncin kotu da sauye-sauyen gudanarwa da suka faru bayan INEC ta fara wallafa jerin ‘yan takara ne suka haifar da wannan yanayi.
Ƙungiyar ta ce irin wannan rashin daidaito na iya jefa masu zaɓe da jami’an tattara sakamako cikin ruɗani yayin kaɗa ƙuri’a da tattara sakamako.
Saboda haka, ta buƙaci INEC ta fito ta yi wa jama’a cikakken bayani kan jerin jam’iyyun da suka shiga zaɓen da kuma dalilan da suka haifar da bambance-bambancen da aka gani a kayan aikin zaɓen.
Fada ya barke a zaben gwamnan Ekiti
A wani rahoton, kun ji cewa magoya bayan jam'iyyun APC da ADC sun yi musayar yawu mai zafi, wacce daga baya ta rikide zuwa fada kan sayen kuri'u a zaben gwamnan jihar Ekiti.
Rahotanni sun nun cewa wani daga cikin magoya bayan ADC ya samu rauni a kai yayin rikicin, inda aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawar likitoci.
Lamarin ya faru ne a a rumfar zabe ta 4, gunduma ta 2 da ke Ilawe Ekiti yayin zaɓen gwamnan jihar Ekiti da ke gudana yau Asabar, 20 ga watan Yuni, 2026.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
