Ana Zargin Mayakan Turji Suna Karbar Horaswar Manya da Sababbin Makamai

Ana Zargin Mayakan Turji Suna Karbar Horaswar Manya da Sababbin Makamai

  • Wasu majiyoyi sun fara zargin cewa mayaƙan da ke biyayya ga rikakken dan ta'adda, Bello Turji na samun horo
  • An ce wasu manyan na hannun damansa suna jagorantar atisayen soja tare da sababbin mayaƙa da makamai masu ƙarfi
  • Wata kungiya ta buƙaci hukumomi su ƙara sa ido tare da binciken bayanan domin dakile duk wata barazana ga rayuka da dukiyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Sababbin rahotanni sun bayyana fargaba game da tabarbarwar rashin tsaro a jihar Sokoto wanda ke da alaka da Bello Turji.

An ce a wasu sassan gabashin Sokoto ana zargin cewa mayaƙan da ke biyayya ga fitaccen ɗan bindiga, Bello Turji, na gudanar da horon amfani da makamai.

Ana fargabar yaran Turji sun fara karbar horon amfani da manyan makamai a Sokoto
Dan ta'adda, Bello Turji da ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

Yankin da aka ce yaran Turji suka taru

Rahoton da Punch ta samu ya ce ana gudanar da horaswan ne a yankunan da suka tashi daga Bingabale Kudu zuwa Bafarawa ta Gabas da Bargaja, kusa da iyakar Sokoto da Zamfara.

Kara karanta wannan

Da gaske yan ta'adda sun harbo jirgin sojojin sama a Niger? Bayanai sun fito

A cewar rahoton, mayaƙan da ke da alaƙa da Turji suna gudanar da atisayen irin na soja tare da amfani da sababbin makaman da aka samu.

Rahoton wanda mai kula da ƙungiyar Movement for Social Justice and Good Governance a Sokoto, Basharu Altine, ya fitar, ya yi zargin cewa wasu manyan abokan Turji na cikin shirin.

Altine ya ce bayanan sirri da ƙungiyarsa ta samu sun nuna cewa mayaƙan suna samun horo kan yadda ake amfani da manyan makamai da aka shigo da su yankin.

Ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa mayaƙan na gudanar da atisayen dabarun yaƙi da koyon amfani da sababbin makamai masu ƙarfi.

Altine ya kuma yi zargin cewa bayanan farko sun nuna an kawo wasu sababbin makamai yankin tare da sababbin mayaƙan da ake zargin suna da alaƙa da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.

A cewarsa, manufar waɗannan mutanen ita ce horar da mayaƙan Turji da kuma ƙarfafa ayyukansu a yankunan kan iyakar Sokoto da Zamfara.

An 'gano' wasu yaran Turji na karbar horon yaki da makamai
Taswirar jihar Sokoto da ke fama da hare-haren yan bindiga. Hoto: Legit.
Source: Original

Kayan da ake zargin an tura wa Turji

Altine ya kuma yi zargin cewa bayanan da aka samu daga Binchi sun nuna na’urorin hangen dare da ake zargin Turji ya samu suna cikin kayan da aka kai sansanoninsa.

Kara karanta wannan

APC ta yi magana da 'yan majalisa suka fara maganar Tinubu ya sauka

Ya ƙara da cewa bincike ya danganta wasu shugabannin ‘yan bindiga biyu, Haru Dole da Ibrahim Chimo, da safarar da sayen waɗannan makamai.

Altine ya ce rahotanni sun nuna cewa Haru Dole da Ibrahim Chimo sun taka muhimmiyar rawa wajen isar da makaman tare da Bello Turji.

Kamar yadda Altine ya wallafa a Facebook, ya kuma yi zargin cewa ana samun ƙarin haɗin kai tsakanin Chimo da Turji, lamarin da ka iya ƙara tsananta matsalar tsaro.

Daga ƙarshe, Altine ya buƙaci hukumomin tsaro su ƙara sa ido da gudanar da bincike mai zurfi domin tabbatar da gaskiyar bayanan.

Gwamna Dauda ya magantu kan kama Turji

An ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi magana kan matakan da suke dauka wajen magance matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.

A jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ce suna cigaba da kokari domin kawo karshen dukkan 'yan ta'addan da ake ganin kamar sun gagara.

Da aka masa tambaya game da kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji, Mai girma gwamnan ya bayyana cewa suna daukar matakin kama shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.