'Ana Boye Gaskiya': Iyalan Sojojin da Suka Shirya Juyin Mulki Sun Nemi Adalci

'Ana Boye Gaskiya': Iyalan Sojojin da Suka Shirya Juyin Mulki Sun Nemi Adalci

  • Iyalan jami’an sojin da ake zargi da shirin juyin mulki sun yi zargin cewa ana tauye hakkinsu tare da rashin gaskiya a shari’ar kotun soji
  • Matan jami’an sun ce an hana wadanda ake tuhuma ganin lauyoyi da iyalansu na tsawon watanni, tare da bayyana damuwar su kan lafiyarsu
  • Iyalan sun bukaci a bude shari’ar ga jama’a da masu sa ido domin tabbatar da gaskiya, adalci da bin ka’idojin da dokar kasa ta tanada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Iyalan wasu jami’an sojin Najeriya da ake tsare da su bisa zargin hannu a shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun bayyana damuwarsu kan yadda ake gudanar da shari’ar kotun soji.

Iyalan sun zargi rundunar sojin da azabtarwa, take hakkin dan Adam da kuma rashin bayyana cikakken bayani game da matakin da ake dauka kan jami’an da aka tsare.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun bindige dan ta'adda mai garkuwa da mutane

Iyalan sojojin da ake tsare da su kan juyin mulki sun nemi a yi masu adalci
Shugaba Bala Tinubu ya na jawabi a wani taro. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Iyalan sojojin da aka kama sun magantu

A yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Juma’a, kakakin matan jami’an da ake tsare da su, Aishatu Yusufu, ta ce sun yanke shawarar yin magana ne saboda suna ganin ana boye wa jama'a gaskiyar lamarin, in ji rahoton The Cable.

Aishatu Yusufu ta bayyana cewa iyalan suna mutunta rundunar soji da dokokinta, amma suna cikin damuwa kan yadda ake mu’amala da ‘yan uwansu tun bayan kama su kimanin watanni tara da suka gabata.

Ta ce su ba ‘yan siyasa ba ne kuma ba masu tayar da hankali ba ne, sai dai iyalai ne da ke neman a tabbatar da adalci ga wadanda ake tuhuma.

“Mu iyalai ne, mata da ‘ya’yan jami’an da ake zargi da shirin juyin mulki. Ba ‘yan siyasa ba ne mu, ba masu tayar da hankali ba ne, kawai muna magana ne don a yi wa mazajenmu, iyayenmu adalci."

Kara karanta wannan

Da gaske yan ta'adda sun harbo jirgin sojojin sama a Niger? Bayanai sun fito

- Aishatu Yusufu.

Ta kara da cewa suna kaunar Najeriya tare da girmama tsarin soji, amma suna fatan a gudanar da shari’ar cikin gaskiya da adalci.

Zargin hana ganawa da lauyoyi da iyalai

Kakakin iyalan ta yi zargin cewa an hana jami’an da ake tsare da su damar ganin lauyoyi da ‘yan uwansu na tsawon sama da kwanaki 180.

A cewarta, wasu daga cikin jami’an sun fuskanci matsalolin lafiya, ciki har da matsalar gani da numfashi, kamar Sahara Reporters ta ruwaito.

Ta ce iyalan sun yi kokarin samun bayanai da damar ziyartar wadanda ake tuhuma amma hakan ya ci tura.

Rokoton da iyalan sojojin suka yi

Iyalan sun bukaci hukumomin soji su bai wa ‘yan jarida da jama’a damar bibiyar yadda shari’ar ke gudana.

Sun kuma nemi a bari kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa su sa ido kan shari’ar tare da ba da damar gudanar da gwaje-gwajen lafiya na daban ga wadanda ake tsare da su.

Kara karanta wannan

N70000 ta yi kadan: NLC za ta sake zama da Tinubu kan sabon mafi karancin albashi

Yusufu ta yi kira ga kasashen duniya da su sanya ido kan lamarin, tana mai cewa adalci ba wai sakamakon karshe na shari’a kadai ba ne, har ma da yadda aka gudanar da ita.

Ta ce ya kamata tsarin shari’a ya kasance mai nuna gaskiya domin tabbatar da amincewar jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com