Neman halal da wuya: Yadda mata ke aikin kwasar yashi a Abuja

Neman halal da wuya: Yadda mata ke aikin kwasar yashi a Abuja

A wani kauye mai suna Chibibiri da ke karamar hukumar Kuje, babbar birnin tarayya Abuja, matan al'ummar Basa sun ce suna fama da talauci da karancin aiki.

Hakan ya sanya su kwasar yashin rafi domin su bai wa masu motar Tifa don samun kudin kashewa.

Sun bayyana cewa da wannan kudi da suke samu ne suke ciyar da iyalansu da kuma kai 'ya'yansu makaranta.

A hira da aka yi da matan sun ce: “Ga shi muna kwashe yashi. Mijina ya mutu ga yara barkatai. Muna fama da kudin abinci da kudin makaranta, ga shi ina shiga rafi ina kwasar yashi, akwai wahala sosai.”

“Ga shi ba ma samun abinci da za mu bai wa yara su ci. Muna da niyyar da za mu sanya yara a makaranta, ba mu da kudi. Idan ba mu shiga rafi don samun kudi ba, ba za mu samu kudin makarantar yara ba."

KU KARANTA KUMA: Kalli Amina Yahaya, shugabar dalibai ta farko mace a jami’ar Usman Danfodiyo

Sun nemi gwamnati ta kawo masu agaji cikin gaggawa.

A wani labari na daban mun ji cewa; Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayar da umurnin dakatar da Direktan Asibitin Zamani ta Umaru Shehu da wasu likotoci hudu da a ba a same su a baki aiki ba lokacin da gwamnan ya kai ziyarar bazata.

Gwamnan jihar ya ziyarci asibitin kwararru na jihar da kuma Asibitin Umaru Shehu misalin karfe 2 na dare inda ya gano cewa dukkan likitocin asibitin 19 ba su nan ciki har da biyu da ke aikin dare domin kulawa da marasa lafiya.

Gwamnan ya bukaci ma'aikatan jinya da ke asibitin su kira likotocin a wayar tarho amma babu wanda ya amsa kirar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel