Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Yan bindiga sun kashe mutum 3, sun sace 6 a Katsina

Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Yan bindiga sun kashe mutum 3, sun sace 6 a Katsina

Yan bindiga a sun kai hari kauyuka hudu a karamar hukumar Batsari dake jihar Katsina a yammacin ranar Lahadi, inda suka kashe mutane uku sannan suka yi garkuwa da mutane shida.

Kauyukan da lamarin ya cika da su, sun hada da Shingi, Sabon Garin Wagini, Hayin Nuhu da Dan Tudun Wagini.

An tattaro cewa a Shingi, an kashe babban limamin kauyen, Malam Abu Garba.

Hakazalika a kauyukan Sabon Garin Wagini an kashe wasu mutane biyu masu suna Husaini Dattijo da Harisu.

An yi garkuwa da matan aure shida sun kuma sace dabbobi a harin da ya dauki fiye da sa’o’i uku.

A lokacin da aka tuntube shi, kakakin rundunar yan sanda reshen jihar, ASP Anas Gewaza ya tabbatar da kisan limamin a Shingi inda ya yi alkawarin ci gaba da tuntuba akan sauran.

KU KARANTA KUMA: NNPC: Bamu da wani asusun sirri, kudinmu na zuwa takanas cikin asusun gwamnatin tarayya ne - Kyari

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa wasu matasa mazauna kauyen Hunki dake karamar hukumar Awe ta jihar Nasarawa sun samu nasarar damke wani mutum wanda ake zarginsa da aikata laifin garkuwa da mutane inda suka hannunta shi ga ‘yan sanda.

An kama wannan mutum ne da zargin cewa yana daya daga cikin wadanda suka taba sace Sarkin Hunki, Malam Muhammadu inda suka nemi a bada naira miliyan hudu kan su sake shi, amma daga bisani suka karbi N600,000 suka sako shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel