"Mijina Yana Kawo Ƴan Mata Ya Kwanta da Su a Gadon Aurenmu," Mata Ta Fada wa Kotu

"Mijina Yana Kawo Ƴan Mata Ya Kwanta da Su a Gadon Aurenmu," Mata Ta Fada wa Kotu

  • Wata mata mai suna Idiah ta maka mijinta Olalekan a kotu a Ibadan, tana neman a raba aurensu saboda zargin rashin kula da iyali da cin zarafi
  • Idiah ta zargi mijinta da watsi da ita da ‘ya’yansu shida, amma, babban zargin shi ne yadda ta ce mijin yake lalata da 'yan matansa a kan gadon aurensu
  • Kotun Gargajiya ta Mapo ta dauki mataki game da mijin, wanda yaki bayyana a gabanta, yayin da aka sanya sabuwar rana don sauraron karar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Oyo – Wata mata mai suna Idiah ta bukaci Kotun Al’ada ta Grade A da ke Mapo, Ibadan, jihar Oyo, ta raba aurenta da mijinta Olalekan bisa zargin rashin daukar nauyi, cin amana da kuma cin zarafi a cikin gida.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu na tsare a gidan yari, IPOB ta rufe ofishin shugaban Biafra

Idiah ta gabatar da korafinta ne a gaban kotun, inda ta bayyana cewa mijinta wanda ya kamata ya kasance mai kula da iyali ya gaza sauke nauyin da ya rataya a kansa.

Wata mata ta kai karar mijinta a kotu ta nemi a raba aurensu
Gudumar da alkalai ke amfani da ita a kotu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Mata ta zargi mijinta da kawo 'yan mata

A cewar matar, Olalekan ya dade yana watsi da ita da ‘ya’yansu shida, inda ya bar musu nauyin kula da rayuwar yau da kullum ba tare da isasshen tallafi ba, in ji rahoton Tribune.

Idiah ta kuma yi zargin cewa mijin nata na kashe kudin da ya samu wajen wasu mata a waje yayin da ya ke kin biyan bukatun gidansa.

Mai karar ta shaidawa kotun cewa mijinta na yawan kawo wasu mata cikin gidansu, har ma tana zargin cewa yana lalata da su a kan gadon aurensu.

Ta ce duk lokacin da ta kalubalanci wannan dabi’a, mijin nata kan mayar da martani ta hanyar cin zarafinta. A cewarta, wannan hali ya sanya ta rayuwa cikin tsoro da rashin kwanciyar hankali.

Ta zargi mijinta da lalata kasuwancinta

Idiah ta kara da cewa mijinta ya kasance yana lalata kayayyakin kasuwancinta a duk lokacin da suka samu sabani.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun bindige dan ta'adda mai garkuwa da mutane

Ta ce wannan dabi’a ta janyo mata asarar kudi har ta kai ga durkushewar kasuwancin da take dogaro da shi wajen kula da ‘ya’yansu.

Baya ga neman raba auren, Idiah ta roki kotun da ta ba ta damar kula da ‘ya’yansu shida.

Ta kuma bukaci kotun ta umarci Olalekan ya ci gaba da daukar nauyin kula da yaran musamman ta bangaren abinci, ilimi da lafiya.

Wata mata a Oyo ta nemi kotu ta raba aurenta da mijinta
Taswirar jihar Oyo, inda wata mata ke neman saki daga kotu. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kotun ta dage sauraron karar

Duk da cewa an aika wa Olalekan sammaci domin ya bayyana a gaban kotu, bai halarci zaman ba, in ji wani rahoto na Punch.

Bayan sauraron bayanan matar, shugabar kotun, Mai shari’a S.M. Akintayo, ta dage karar tare da umartar a sake fitar da sanarwar sauraron shari’a domin a kai wa wanda ake karar.

Za a ci gaba da sauraron karar ne bayan an tabbatar da cewa an sanar da Olalekan bisa ka’ida.

'Mijina ya daina kwana da ni' - Mata a kotu

A wani labari, mun ruwaito cewa, an ga abin mamaki a wata kotu a Ilorin yayin da matar aure, Aminat ta fashe da kuka kan abubuwan da mijinta ke mata a gidan aure.

Kara karanta wannan

An fallasa shirin shawo kan talaka da shinkafa da taliya a zaben gwamnan Ekiti

Matar ta shaida wa alkali cewa mijinta mai suna, Isma'il Gobir, ya ƙauracewa gadon sunnah, ba ya kula da ita da yaran da suka haifa.

Sai dai magidancin ya ce har yanzu yana da sha’awar son zaman aure da Aminat, kuma ya roki a ba shi lokaci domin ya samu damar sasantawa da matarsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com