Abdulaziz Yari Ya Shirya Daukar Nauyin Zanga Zangar Adawa da Tinubu? Gaskiya Ta Fito
- Kafofin sadarwa sun cika da wasu rahotanni da ake yaɗawa game da tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari
- Sanata Yari ya yi karin haske kan zargin cewa yana daukar nauyin zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
- Babban mai taimaka masa, Abdullahi Tsafe, ya ce Yari ya dade yana goyon bayan Tinubu tun kafin ya zama shugaban kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari, ya yi martani kan zargin ɗaukar nauyin zanga-zangar adawa da Bola Tinibu.
Abdulaziz Yari ya nesanta kansa daga wata zanga-zangar da ake shirin yi domin nuna adawa da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Twitter
Hadimin Abdulaziz Yari ya karyata jita-jitar zanga-zanga
Babban mai taimaka masa a bangaren sadarwa, Abdullahi Tsafe, ya bayyana a wata sanarwa da ya wallafa a shafin Facebook.
Sanarwar ta bayyana cewa zargin da ke cewa Yari na daukar nauyin ko tallafa wa zanga-zangar adawa da gwamnati karya ne.
Tsafe ya bayyana zargin a matsayin marar tushe, mai cike da shirme wanda aka shirya saboda dalilan siyasa, yana mai cewa Yari ba shi da wata alaka da zanga-zangar.
Ya ce:
“A bayyana karara ne cewa Sanata Abdulaziz Abubakar Yari ba shi da wata alaka ko kadan da duk wata zanga-zangar da ake shirin yi."
Ya kara da cewa zargin ya samo asali ne daga masu yada bayanan karya da kuma kokarin bata sunan dan siyasar.
A cewarsa, babu wani dalili da zai sa Yari ya dauki nauyin zanga-zanga kan gwamnatin da ya dade yana goyon baya tare da taimakawa wajen karfafa ta.

Source: Facebook
Dangantakar Yari da Shugaba Bola Tinubu
Tsafe ya ce dangantakar Yari da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ginu ne bisa mutunta juna, akida ta siyasa da kuma kudurin ganin Najeriya ta samu ci gaba da kwanciyar hankali.
Ya bayyana cewa Yari ya mara wa burin Tinubu na zama shugaban kasa baya tun kafin nasararsa, inda ya zuba dimbin albarkatu da karfin siyasa domin cimma hakan.

Kara karanta wannan
An bukaci Shugaba Tinubu ya ayyana wani shirin watanni 6 don magance matsalolin Najeriya
Sanarwar ta ce Tinubu ya sha yabawa Abdulaziz Yari a bainar jama’a saboda biyayyarsa, goyon bayansa da gudummawar da ya bayar ga nasarar jam’iyyar APC.
Tsafe ya ce ba zai yiwu mutum da ya bayar da irin wannan gudummawa ya juya ya fara tallafa wa zanga-zangar da za ta iya raunana gwamnati ba.
Ya kuma zargi masu yada labarin da kokarin bata sunan Yari da kuma yada bayanan da ba su da tushe.
A cewarsa, Yari mutum ne mai kishin kasa wanda bai taba shiga harkokin neman daukaka ta hanyar dabarun siyasa marasa kyau ba.
Sanata Yari ya fadi tasirin APC a Arewa
A baya, an ji cewa Sanata AbdulAziz Abubakar Yari ya nuna jin daɗinsa kan sauya sheƙar da sanatocin PDP guda uku suka yi zuwa jam'iyyar APC.
Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya bayyana cewa sauya sheƙar ta su alama ce da ke nuna ƙarfin da APC take da shi a Arewacin Najeriya.
Dan majalisar ya kuma musanta zargin da ake yi na cewa ana ƙoƙarin maida Najeriya ƙarƙashin jam'iyya ɗaya a mulkin Bola Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
