Wani dan bautar kasa ya ja hankalin NYSC bayan an biya shi alawus sau biyu a wata guda

Wani dan bautar kasa ya ja hankalin NYSC bayan an biya shi alawus sau biyu a wata guda

- Wani dan bautar kasa ya ja hankalin hukumar NYSC kwanan nan bayan ya samu alawus sau biyu a wata guda

- Matashin mai suna Muhammad Abubakar ya wallafa hotunan sakon shigar kudi cikin asusunsa a shafinsa a Twitter

- Yan Najeriya da dama sun jinjina wa Muhammad akan kasancewa wani ‘wakilin chanji’

Wani dan bautar kasa mai suna Muhammad Abubakar ya burge yan Najeriya kwanan nan bayan yayi wani bajinta na nuna gaskiya. Matashin, wanda ya samu alawus sau biyu a wata guda, ya ja hankalin hukumar bautar kasa (NYSC) bayan an biya shi kudin watan Juli har sau biyu.

A cewar Muhammad, ya samu alawus dinsa na Yuli wanda ya kasance N19,800 da safiyar ranar Laraba, 31 ga watan Yuli, sai ya cire kudin daga asusunsa. Sannan da yammacin wannan rana, sai ya kara jin shigar kudi kuma.

Ba tare da kudirin son hamdame Karin kudin da aka yi masa ba, Muhammad ya sanar da hukumar NYSC a shafin Twitter ta hanyar sanya alama da sunansu a shafin nasa. A ruutun da ya wallafa, yayi bayanin halin da ake ciki sannan ya wallafa hotunan sakon shigar kudin asusunsa domin kafa hujja.

KU KARANTA KUMA: An bayyanawa kotun zabe cewa Buhari ya yi jarrabawar WAEC

Kalli yadda ya wallafa a shafin nasa:

Yan Najeriya da dama sun jinjina wa Muhammad akan kasancewa wani ‘wakilin chanji’. Sai dai wasu sun yi kokarin yi masa bayani cewa alawus dinsa na watan Agusta ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel