Abin Tausayi: Dan Kasuwa Ya Mutu a Wani Yanayi a Dakin Fitacciyar 'Yar TikTok a Jihar Kano
- Wani matashin ɗan kasuwa, Isma’il Makaye, ya mutu a gidan budurwarsa yar TikTok, Fati Cele da ke Danbare a jihar Kano
- Abokan mamacin sun yi zargin cewa an ga raunuka a kansa kafin birne shi, amma dai babu wani bayani kan yanayin da ya rasu
- Rundunar 'yan sandan Kano ta fara gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar Isma'il Makaye yayin da ake jiran cikakken bayani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Matashin ɗan kasuwa mai suna Isma’il Makaye ya mutu a wani yanayi da har yanzu ba a tantance ba a gidan budurwarsa, fitacciyar yar TikTok da aka fi sani da Fati Cele.
Rahotonnni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a gidan Fati Cele da ke a unguwar Danbare, karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: An rushe katafaren gidan kasurgumin mai garkuwa da mutane da aka cafke a Edo

Source: Twitter
Daily Trust ta ruwaito cewa Isma'il Makaye, wanda ke harkar kasuwancin kayan kwalliya a yankin Hotoro Tishama, ya rasu ne a safiyar ranar Juma’a, lamarin da ya sa 'yan sanda fara bincike.
Yadda aka dauko gawar Isma'il Makaye
Wani abokin marigayin mai suna Hassan Mohammed, wanda ya ce yana cikin wadanda suka je wurin tare da jami’an ‘yan sanda, ya ce lokacin da suka isa gidan sun tarar da gawar matashin.
A cewarsa, daga bisani an kai gawar mamacin Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad kafin a tura ta zuwa Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Ya ce:
“Mun same shi ya riga ya mutu lokacin da muka isa wurin tare da ‘yan sanda. Da farko mun je Asibitin Murtala Muhammad, daga bisani kuma aka kai shi Asibitin Abdullahi Wase inda aka tabbatar da rasuwarsa.”
Ana zargin akwai raunuka a kansa
Hassan ya kara da cewa Makaye da Fati Cele sun shafe sama da shekaru biyu suna soyayya kafin su rabu na wani lokaci bayan mamacin ya yi aure, daga bisani kuma suka sake sulhu.
Ya bayyana cewa an samu wayoyin mamacin da kuma mukullan motarsa a wurin da lamarin ya faru, kamar yadda Leadership ta ruwaito..
Har ila yau, ya yi zargin cewa an ga raunuka a kan mamacin, yana mai cewa akwai alamun zubar jini har lokacin da aka yi masa jana’iza.
“Akwai raunuka a kansa, kuma muna zargin wata kila an bugi kansa da wani abu,” in ji shi.

Source: Original
An yi jana'izar Isma'il Makaye
An yi jana’izar Isma’il Makaye a ranar Juma’a a Unguwa Uku Yan Awaki bisa koyarwar addinin Musulunci.
Fati Cele, wadda ta fito daga jihar Borno, ta shahara ne a TikTok ta hanyar bidiyoyin nishadi da raye-raye da take yi a yankin Sabon Gari da ke Kano.
Zuwa lokacin hada wannan rahoto, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai amsa kiran waya da aka yi masa domin jin ta bakinsa ba.
Budurwa ta mutu a dakin saurayinta
A wani labarin, kun ji cewa wani saurayi a birnin Abuja ya shiga tashin hankali bayan mutuwar budurwarsa yayin da ta kawo masa ziyara na musamman.
Wani mazaunin yankin mai suna Dauda ya bayyana cewa Esther ta baro gida lafiya kalau domin ziyartar saurayinta amma aka kira yayanta aka ce masa ta mutu.
Dauda ya ce saurayin ya bayyana masa cewa ya saya wa Esther abinci lokacin da ta kawo masa ziyara, amma bayan ta ci abincin sai ta fara amai.
Asali: Legit.ng
