Yanzu Yanzu: Kotu ta ba EFCC izinin daskarar da asusun Bauchi

Yanzu Yanzu: Kotu ta ba EFCC izinin daskarar da asusun Bauchi

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Litinin, 5 ga watan Agusta ta amince da rokon hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) na daskarar da asusun bankin First City Monument Bank (FCMB) mai lamba 0998552074 na gwamnatin jihar Bauchi.

Taiwo Taiwo, alkalin kotun, ya bukaci EFCC da ta sanar da wanda abun ya shafa umurnin cikin kwanaki 21.

Ya kuma dage shari’an zuwa ranar 3 ga watan Satumba.

A wani labarin kuma, mun ji cewa jami’an hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC sun kai wani samame gidan tsohon gwamnan jahar Zamfara, Abdul Aziz Yari, dake garin Talatar Mafara domin gudanar da bincike.

KU KARANTA KUMA: Shehu Sani yayi martani bayan kotu ta bayar da belin El-Zakzaky zuwa kasar waje domin magani

Legit.ng ta ruwaito shaidun gani da ido sun bayyana cewa jami’an hukumar da yawansu ya kai mutum 20 sun dira gidan tsohon gwamnan ne da misalin karfe 6 na yammcin Lahadi, inda suka kai har zuwa karfe 11 na dare suna bincike.

Haka zalika an jiyo mazauna garin Talatar Mafara da suka yi cincirindo a kofar gidan suna kabarkarin ‘Allahu Akbar’ yayin da jami’an hukumar EFCC suka gudanar da binciken nasu, da nufin nuna adawarsu da abinda EFCC ke yi ma tsohon gwamnan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel