Trump Ya Yi Magana kan 'Harin Amurka' da Ya Kashe Yara 'Yan Makaranta 170 a Iran

Trump Ya Yi Magana kan 'Harin Amurka' da Ya Kashe Yara 'Yan Makaranta 170 a Iran

  • A farkon yakin Amurka da Iran an kashe wasu yara 'yan yara makaranta 170 a Jamhuriyar Musulunci ta Iran
  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa babu wanda ya farmaki makarantar da gangan lokacin kai harin
  • Donald Trump ya nuna cewa yaki abu ne mai muni bayan alamu sun nuna cewa dakarun Amurka ne suka kai hari a makarantar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Paris, Faransa - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan harin da ake zargin Amurka ta kai wanda ya kashe yara 'yan makaranta a Iran.

Shugaba Trump ya bayyana cewa babu wanda ya kai hari da gangan wata makarantar 'yan mata ta ƙasar Iran inda aka kashe fiye da yara da malamai 170 lokacin wani harin makami mai linzami a ranar farko ta fara yaƙin.

Kara karanta wannan

"Yan hassada ne": Trump ya hasala kan masu sukar yarjejeniyar Amurka da Iran

Trump ya yi magana kan harin Amurka a Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, a fadar White House Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Sky News ta kawo rahoton cewa Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a wajen taron G7 a Faransa a ranar Laraba, 17 ga watan Yunin 2026.

An kashe dalibai da malamai a Iran

Hukumomin Iran sun bayyana cewa sama da ɗalibai da malamai 175 ne suka rasa rayukansu bayan da aka farmaki makarantar firamare ta Shajareh Tayyebeh da ke Minab ranar 28 ga watan Fabrairun 2026.

Wani bincike mai zaman kansa da aka gudanar ya tabbatar da mutuwar mutane 152 sakamakon harin.

Ta hanyar amfani da hanyoyin samun bayanai da dama, an tantance sunayen daukacin ɗalibai 120 da aka kashe, waɗanda shekarunsu ke tsakanin shida zuwa 13, da kuma malamai 26.

Ana zargin Amurka da kai harin

Shugaban na Amurka ya taɓa zargi ba tare da gabatar da wata shaida ba, cewa Iran ce ke da alhakin kai harin.

Sai dai, daga baya ya bayyana cewa ba shi da isassun bayanai game da harin, inda ya lura cewa ana nan ana gudanar da bincike kuma zai karbi sakamakon binciken da zarar an fitar da shi.

Kara karanta wannan

A karshe, Trump ya amince Iran ta mallaki makamai masu karfin gaske

Ana zargin Amurka sosai da kai wannan hari, yayin da ƙarin shaidu ke nuna cewa tsofaffin bayanan sirri na Amurka ne “wataƙila” suka yi sanadiyyar kai harin a kan makarantar.

Trump ya yi magana kan kashe yara 'yan makaranta 170 a Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

Me Trump ya ce kan harin?

Yayin da yake magana da manema labarai, Trump ya yi watsi da tambayoyin da ke cewa ko akwai wanda zai fuskanci hukunci kan lamarin, inda ya bayyana binciken da wani abu da ba a saba gani ba, tashar Reuters ta kawo rahoton.

“Abu ne mai ban mamaki a yi irin wannan tambayar a wannan lokaci, domin kuna magana ne a kan abin da ya faru tuntuni. Babu wanda ya yi hakan da gangan”.
“Ana tafka kura-kurai, yaƙi abu ne mai muni… Zan yi wa Pete Hegseth (Ministan tsaron Amurka) wannan tambayar, domin suna gudanar da bincike a kai."

- Shugaba Donald Trump

Trump ya soki masu sukar yarjejeniya da Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya ragargaji masu sukarsa kan yarjejeniyar da ya kulla da Iran.

Yarjejeniyar dai ta sanya wasu suna cewa sharuɗɗan kamar sun ƙarfafa ikon Tehran ne saboda abubuwan da ke kunshe a cikinta.

Shugaba Trump ya ce waɗanda ke tunanin bai matsawa Iran sosai ba ko dai “masu hassada, miyagun mutane ko kuma wawaye.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng