Dubu ta Cika: An Rushe Katafaren Gidan Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane da Aka Cafke a Edo
- Rundunar tsaro ta jihar Edo (ESSS) ta cafke wani jagoran kungiyar masu garkuwa da mutane da ya addabi jama'a a yankin Uromi da kewaye
- Gwamnatin Edo ta jagoranci rushe gidan mutumin, wanda ake zargin ana amfani da shi wajen aikata laifuffukan garkuwa da mutane
- Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka yana hannun yan sanda domin gudanar da cikakken bincike kafin daukar mataki na gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo, Nigeria - Rundunar Tsaron Jihar Edo (ESSS) ta kama wani da ake zargi da kasancewa shugaban ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ta addabi al'umma.
Bayanai sun nuna cewa wanda ke zargin na da alaka da hare-haren garkuwa da mutane da dama a Uromi da wasu yankunan da ke kewaye da ita a Mazabar Sanatan Edo ta Tsakiya.

Source: Original
An mika wanda ake zargi ga 'yan sanda
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa wanda ake zargin, mai suna Christian Okoduwa, na tsare a hannun ’yan sanda a birnin Benin yayin da bincike ke ci gaba.
A wani mataki kuma, gwamnatin Edo ta rushe gidansa da ke kan titin Thursday Street, kusa da titin Amedokhian a Uromi, ƙaramar hukumar Esan North East, bayan samun bayanan sirri da kuma binciken da aka gudanar.
Gwamnati ta rushe gidan Okoduwa
Da yake jawabi yayin rushe ginin, shugaban Rundunar Tsaron Jihar Edo, Barrista John Izegaegbe, ya ce bincike ya nuna cewa ana zargin Okoduwa da hannu a wasu jerin ayyukan garkuwa da mutane da suka addabi yankin Uromi.
Ya ce ana zargin wanda ake tsare da shi yana shigo da wasu mutane daga maƙwabtan jihohi zuwa Uromi domin aiwatar da ayyukan satar mutane.
A cewarsa, da dama daga cikin waɗanda aka kama sun ambaci sunan Okoduwa yayin bincike, inda suka danganta shi da ayyukan garkuwa da mutane a yankin.
“Yawancin waɗanda aka kama sun ambaci sunansa tare da danganta ayyukan garkuwa da mutane da shi. Wannan ne ya sa aka ɗauki matakin rushe gidansa da ke Amedokhian,” in ji shi.
Gwamnatin Edo ta yi gargaɗi
Izegaegbe ya ƙara da cewa duk mutanen da aka kama a Uromi da yankunan da ke kewaye suna da alaka da wanda ake zargin da kuma ƙungiyarsa, cewar rahoton The Nation.
“Bincike ya nuna cewa shi ne ke da hannu a wasu daga cikin manyan laifukan garkuwa da mutane da aka samu a Uromi, kuma yanzu doka ta cimma shi,” in ji shi.

Source: Twitter
Dalilin rushe gidan wanda ake zargi
Sakataren ya bayyana cewa an rushe ginin ne bisa manufar gwamnatin jihar Edo da ta haramta amfani da kadarori wajen aikata laifuffuka.
Ya jaddada cewa duk wani gida ko gini da aka tabbatar ana amfani da shi wajen ayyukan laifi, musamman garkuwa da mutane, za a rushe shi.
'Yan sanda sun kashe ɗan garkuwa
A wani labarin, kun ji cewa rundunar ‘yan sandan Jihar Edo ta kashe wani da ake zargin babban mai garkuwa da mutane ne.

Kara karanta wannan
Kotu ta yi hukunci za a rataye jagoran dabar yan bindiga Jibrin Halilu har lahira
Bayan kashe shi har lahira, 'yan sanda sun sanar da kama wani da ake dangantawa da sace wata mata a wata kasuwa da ke Benin City.
Rahoto ya nuna cewa an ƙwato mota, bindiga, harsasai biyu da tsabar kudi Naira miliyan 2.25 da kuma babur daga wajen wana aka kama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

