Bayan Kisan Rabe, an Yaɗa Cewa an Kashe Babban Kwamanda, Sojoji Sun Yi Martani
- Sojojin Najeriya sun yi karin haske game da jita-jitar cewa yan bindiga sun yi ajalin wani babban kwamanda
- Rundunar ta musanta rahotannin da ke yawo cewa Laftanar Kanal Emmanuel Gabriel Okoye ya mutu a harin ‘yan bindiga
- Hedikwatar Rundunar Soji ta 6 Brigade ta bayyana cewa marigayin kwamandan bataliya ta 20 ya rasu ne bayan rashin lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hedikwatar Rundunar Soji ta 6 Brigade ta Najeriya da Sashen 3 na Operation Whirl Stroke (OPWS), ta yi magana bayan mutuwar kwamandanta.
Rundunar sojoji ta musanta rahotannin da ke alakanta mutuwar marigayi kwamandan Bataliya ta 20 Model da ke Serti a Taraba a hannun ƴan bindiga.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa da mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar, Laftanar Umar Muhammad, ya fitar, cewar Leadership.
Jita-jitar da ake yadawa kan kwamandan sojoji
Wasu sun yi ta yada labarin cewa Laftanar Kanal Emmanuel Gabriel Okoye ya mutu a harin ‘yan bindiga.
Rundunar ta bayyana rahotannin a matsayin marasa tushe, marasa inganci kuma masu yaudarar al'umma.
Sanarwar ta ce Laftanar Kanal Okoye ya rasu ne a ranar 13 ga Yunin 2026 bayan ya yi gajeruwar rashin lafiya, ba kamar yadda wasu suka yi ikirari ba.
Ta ce:
“Domin kawar da duk wata shakka, Laftanar Kanal Emmanuel Gabriel Okoye ya rasu ne a ranar 13 ga Yunin 2026 bayan gajeruwar rashin lafiya.
“Mutuwarsa ba ta da alaka da harin ‘yan bindiga ko wani lamari da ya shafi aiki, kamar yadda wasu rahotannin kafafen sada zumunta suka yi nuni.”

Source: Original
Mutuwar kwamanda: Gargadin sojoji kan yada karya
Rundunar ta bayyana cewa an riga an tabbatar da yadda mutuwar jami’in ta faru kuma an sanar da hakan ta hanyoyin hukuma da suka dace.
Ta kuma gargadi jama’a kan yada bayanan da ba a tabbatar da su ba da kuma hasashe marasa tushe da ka iya haifar da rudani,cewar Daily Post.

Kara karanta wannan
Jerin gwamnonin jihar Ekiti daga 1999 zuwa yau yayin da ake shirin sabon zabe a 2026
Sanarwar ta nuna damuwa cewa irin wadannan labaran karya na iya jefa jami’an soji, iyalansu da sauran jama’a cikin fargaba da rashin tabbas.
Har ila yau, rundunar ta ce yada rahotannin da ba su da tushe game da mutuwar babban jami’in sojin rashin nuna tausayi ne ga iyalansa tare da rashin girmama tarihinsa.
Saboda haka, rundunar ta bukaci ‘yan jarida da sauran jama’a su rika dogaro da bayanan da hukumomin da suka dace suka tabbatar kafin yada su.
Ta ce:
“Muna shawartar jama’a da masu aikin yada labarai da su yi watsi da wadannan rahotanni masu yaudara tare da gujewa yada bayanan da ba a tabbatar da su ba.”
Janar Rabe ya mutu a hannun yan bindiga
Kun ji cewa Gwamnatin Katsina ta tabbatar da rasuwar tsohon Manjo Janar na rundunar sojojin Najeriya, Rabe Abubakar (mai ritaya).
Tsohon sojan ya rasu ne yayin da yake tsare a hannun ‘yan bindiga sakamakon matsalolin ciwon sukari da hawan jini da yake fama da su
Gwamna Dikko Radda ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga jihar Katsina da Najeriya baki daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
