Dalilai 3 da za Su Iya Sanya APC Lashe Zaben Gwamnan Ekiti na 2026
- Mazauna Jihar Ekiti za su kada ƙuri'a a ranar Asabar, 20 ga Yuni, 2026, domin zaɓen gwamna, inda sama da masu jefa ƙuri'a miliyan 1 suka yi rajista
- Gwamna mai ci, Biodun Oyebanji na jam’iyyar APC, na neman wa’adi na biyu a yayin da yake samun gagarumin goyon baya da amincewar ‘yan siyasa daban-daban
- Ana hasashen cewa tsarin APC a matakin ƙasa da wasu abubuwa za su ƙara wa jam'iyyar damar samun nasara a zaɓen gwamnan da ke tafe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ekiti - Daga ƙarfe 8:30 na safiyar Asabar, 20 ga Yuni, mazauna Ekiti za su yi layi a rumfunan zaɓe 2,445 domin zaɓar gwamnan jihar.
Bisa ga jerin sunayen ‘yan takara da hukumar INEC) ta fitar, sama da masu jefa ƙuri’a miliyan 1 ne suka yi rajista domin shiga tsarin zaɓen.

Source: Facebook
A wannan rahoto, Legit Hausa ta bayyana dalilai uku da za su iya bai wa jam’iyyar APC nasara a zaɓen gwamnan jihar Ekiti na 2026.
Me zai iya ba APC nasara a Ekiti?
1. Ƙarfin kasancewa a kan mulki
Ana ganin karfin kasancewa a kan mulki zai taimakwa jam'iyyar APC a Ekiti, inda wasu ke ganin cewa nuna ayyukan da gwamnan ya yi a baya za su taimaka masa.
Bisa yadda yanayin siyasar Najeriya ke gudana, yawanci wadanda ke kan mulki a matakin kasa ko jiha na samu damar tazarce a kan 'yan adawa.
2. Goyon bayan da APC ke samu
APC ta bayyana cewa tana samun ƙarin ƙarfi a jihar Ekiti sakamakon yawan goyon bayan da take samu a wajen 'yan siyasa da jama'a.
Alal misali, tun daga shekarar 2023, tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya nuna goyon bayansa ga Gwamna Biodun Oyebanji domin ya sake yin wa’adi na biyu, yana mai yabawa salon shugabancinsa da ci gaban da ya samar.

Kara karanta wannan
Zaben fitar da gwani: APC ta yi martani bayan tsohon sufeta janar ya fice daga cikinta
A watan Yuli, 2025, Fayose, wanda mamba ne na jam’iyyar PDP, ya bayyana goyon bayansa a bainar jama’a ga ci gaba da mulkin Oyebanji a wani gangamin APC da aka gudanar a Ado-Ekiti, duk da kasancewarsa ɗan jam’iyyar adawa.
Jaridar The Punch ta ruwaito Fayose yana cewa:
“Na bayyana a bainar jama’a, ba tare da wata shakka ba, goyon bayana ga Shugaba Bola Tinubu domin ya sake yin wa’adi na biyu.
"Haka kuma, ina goyon bayan gwamnanmu, Biodun Oyebanji, da mataimakinsa domin su sake yin wa’adi na biyu.”
Hakazalika, duk da kasancewarsa mai sukar gwamnatin tarayya mai ci, tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, ya nuna goyon bayansa ga Oyebanji.

Source: Facebook
Ya riga ya bayyana goyon bayansa ga ɗan takarar APC, yana mai cewa gwamnan ya yi aiki mai gamsarwa kuma ya cancanci a ba shi goyon baya domin ci gaba.
Fayemi ya ce, kamar yadda The Nation ta ruwaito:
“Abin da nake cewa shi ne, ni da dukan iyalina muna goyon bayan wa’adi na biyu na Biodun Abayomi Oyebanji.
“Dukanmu mun amince cewa gwamnanmu mutum ne mai halaye nagari wanda ya yi aiki matuƙa cikin shekaru biyu da suka gabata. Kuma mun yarda cewa idan muka mara masa baya a matsayin ɗan takararmu, mutanen Ekiti za su bi mu cikin farin ciki. Saboda haka, abin da ya fi dacewa shi ne mu goyi bayan shi domin ya ci gaba da kyakkyawan shugabanci har zuwa shekarar 2030.”
Rahotanni daga Ekiti sun nuna cewa ɗimbin manyan ƙungiyoyin siyasa a jihar su ma sun nuna goyon bayansu ga APC da Gwamna Oyebanji.
3. Tsarin APC a matakin ƙasa
Masu nazarin siyasa da sakamakon ra’ayoyin jama’a sun amince cewa APC na da babbar fa’ida ta fuskar tsari a zaɓen gwamnan Ekiti na 2026.
Wannan ya samo asali ne daga zurfin alaƙar Gwamna Oyebanji da jama’a a dukkan ƙananan hukumomi 16 na jihar da kuma gundumomi 177.

Source: Facebook
Yiaga ta yi korafi a zaben Ekiti
A wani labarin, kun ji cewa jami'ar Yiaga Africa, Safiya Bichi ta ce jita-jitar sayen ƙuri’u da yaɗa bayanan ƙarya na iya tauye sahihancin zaɓen gwamnan Ekiti.
Da take magana da manema labarai, Bichi ta ce rahotannin da ke nuna cewa ‘yan siyasa suna raba kayan abinci da kuɗi ga mazauna jihar sun yawaita gabanin zaɓen ranar Asabar.
Ta ce Yiaga Africa ta kuma ji zarge-zargen cewa wasu ‘yan siyasa suna biyan masu jefa ƙuri’a kuɗi tun kafin zaɓe tare da yin alƙawarin kammala biyansu bayan zabe.
Asali: Legit.ng

