'Yan Sanda Sun Fadi Wasu Matakai da Suka Dauka da Aka Fara Zaben Gwamnan Ekiti
- Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gargadi masu shirin karya dokokin zabe a Ekiti, tana mai cewa za a hukunta duk wanda ya sabawa doka
- An kammala tura jami’an tsaro zuwa rumfunan zabe 2,545 da muhimman wurare domin tabbatar da zaman lafiya yayin zaben gwamna
- Sufeto Janar na ‘yan sanda Tunji Disu ya bukaci jami’an da aka tura su yi aiki cikin kwarewa yayin da rundunar ta jero laifuffukan zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Ekiti – Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gargadi duk wanda zai yi yunkurin kawo cikas ga zaben gwamnan jihar Ekiti da cewa zai fuskanci hukunci bisa tanadin dokokin kasar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Anthony Placid, ya fitar ranar Juma’a, ‘yan sandan sun ce za a dauki matakin da ya dace kan duk wani wanda zai aikata laifin da zai iya lalata sahihancin tsarin zaben.

Source: Facebook
An tura jami'an tsaro sassan Ekiti
Rundunar ta bukaci masu kada kuri’a da sauran masu ruwa da tsaki su kasance masu bin doka tare da gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali a lokacin zaben, in ji rahoton Channels TV.
A cewar Placid, rundunar ta kammala cikakken shirin tura jami’an tsaro da kayan aiki domin zaben gwamna na Ekiti.
Ya bayyana cewa shirin tsaron ya shafi dukkan rumfunan zabe 2,545 da ke fadin jihar, da kuma muhimman wurare kamar cibiyoyin gwamnati, hanyoyin shiga da fita, kan iyakokin al’umma da sauran wurare masu muhimmanci.
Ya ce an shirya wannan tsarin tsaron ne domin tabbatar da tsaron masu kada kuri’a, ma’aikatan zabe, masu sa ido da kuma kayayyakin zabe.
Matakan tsaro da 'yan sanda suka dauka
Kwamishinan ‘yan sanda mai kula da tsaron zabe, Shogule Abayomi, ya ce an samar da wani tsari mai karfi na tsaro domin tabbatar da zaben ya kasance cikin lumana, gaskiya da inganci.

Kara karanta wannan
An jibge jami'an tsaro, sun hana mutane zirga zirga a kananan hukumomi 2 a jihar Kano
Ya ce an rarraba jami’an tsaro da kayayyakin aikinsu zuwa wuraren da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyi tare da tabbatar da gudanar da zaben cikin nasara.
Sufeto Janar na ‘yan sanda, Tunji Disu, ya tabbatar wa jama’a cewa duk jami’an da aka tura domin aikin zabe sun samu cikakken bayani kan nauyin da ke kansu da kuma ka’idojin gudanar da aiki.
'A guji yada bayanan karya' - 'Yan sanda
‘Yan sandan sun yi kira ga masu kada kuri’a da su fito cikin kwanciyar hankali domin amfani da hakkinsu na zabe ba tare da tsoro ko barazana ba.

Source: Original
Haka kuma, rundunar ta gargadi jama’a kan yada bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, tana mai cewa irin wadannan bayanai na iya haifar da rudani ko kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sake jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Ekiti tare da tabbatar da gudanar da zabe mai inganci, adalci da zaman lafiya.
Duba bayanai kan laifuffukan zabe da 'yan sanda suka wallafa a shafinsu na X a kasa:
Asali: Legit.ng

