Buhari yace ambatan sunan wanda zai gaje shi a 2023 zai haifar masa da matsaloli

Buhari yace ambatan sunan wanda zai gaje shi a 2023 zai haifar masa da matsaloli

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 30 ga watan Yuli, yace ba zai ambaci sunan wanda zai gaje shi ba a 2023

- Kungiyar Pro-Acad ta bukaci shugaban kasar da ya fara horar da wani matashi da zai maye gurbinsa idan ya gama wa’adinsa na biyu a 2023

- Buhari ya bayyana cewa nuna wani a matsayin wanda zai gaje shi zai haifar masa da matsaloli

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 30 ga watan Yuli, yace ba zai ambaci sunan wanda zai gaje shi ba a 2023.

Buhari yayi magana ne yayinda ya karbi bakuncin mambobin kungiyar Progressives in Academics (Pro-Acad) a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kungiyar ta bukaci shugaban kasar da ya fara horar da wani matashi da zai maye gurbinsa idan ya gama wa’adinsa na biyu a 2023.

Buhari ya bayyana cewa nuna wani a matsayin wanda zai gaje shi zai haifar masa da matsaloli.

Ya kuma yi gargadin cewa kada wanda yayi tunani cewa zai iya zama shugaban kasa a dare daya.

KU KARANA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da dukkanin zababbun ministoci 43

Da yake tunawa da kayen da ya sha sau uku, ya bayyana cewa kafin mutum ya zama shugaban kasa sai ya yi aiki sosai.

Shugaban kasar ya kuma ga laifin gwamnatocin jiha akan tsarin almajiri a kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel