Buhari ya zabi mutanen kwarai a matsayin ministoci – Dan majalisa

Buhari ya zabi mutanen kwarai a matsayin ministoci – Dan majalisa

Shugaban masu rinjayi a majalisar dokokin jihar Sokoto, Alhaji Bello Isa Ambarura yace Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabi mutane masu mutunci na hakika a matsayin mambobin sabuwar majalisarsa.

Yayin da yake magana a Sokoto, Ambarira ya bayyana cewa wadanda aka zaba sun kasance kwararru a fannin fasaha sannan kuma gwanaye wadanda an gwada su sannan kuma an tabbatar da hakan.

A kan wanda aka nada daga jihar Sokoto, yace, “Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi ya kasance zabin da ya dace da jihar Sokoto.”

Yace Dingyadi da sauran wadanda aka nada sun kasance da shaidan kwarai, masu kishin kasa kuma masu yiwa kasa hidima.

Ya ba da tabbacin cewa mambobin jam’iyyar APC a majalisar dokokin jihar za su yi aiki tare da shugabanni, mambobin majalisar dokoki na tarayya, karkashin jagorancin Shugaban jam’iyyar a jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, domin janyo hankalin tarayya sosai zuwa ga jihar Sokoto baki daya.

KU KARANTA KUMA: Da zafi-zafi: Ana harbe-harbe yayinda yan sanda ke fatattakar masu zanga-zangar juyin juya hali a Lagas

A halin da ake ciki, ana sanya ran Shugaba Muhammadu Buhari zai rantsar da sabbin ministoci 43 da Majalisar dattawa ta tantance a ranakun 15 da 16 ga watan Agusta a Abuja.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Gida Mustapha ne ya bada wannan sanarwar a wani zance da ya fitar ranar Juma’a.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel