Kada yan Najeriya su sa ran ganin wani abun kirki daga zababbun ministocin Buhari – Galadima da Dantiye

Kada yan Najeriya su sa ran ganin wani abun kirki daga zababbun ministocin Buhari – Galadima da Dantiye

Wani tsohon aminin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda a yanzu ya kasance magoyin bayan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Buba Galadima, ya shawarci yan Najeriya da kada su tsammaci wani abun a zo a gani daga zababbun ministoci, cewa Najeriya ba za ta ga wani abun kirki ba a karkashin wannan shiri na yanzu.

Yayin da yake hira ta wayan talho da jaridar The Guadian a Abuja yace, “Mutum zai yi magana ne kawai akan tantance ministoci bisa ka’ida a mulkin damokradiyya, amma a mulkin mallakar damokradiyya inda mutane ke amfani da sojoji wajen zabar kansu zuwa kan kujerar mulki, kada ka yi tunanin cewa wani abu mai inganci zai faru.

“Idan da ace an gudanar da tantancewar bisa ka’ida, da za mu iya sanya ran ganin wani abu mai ma’ana da amfani, amma kun san cewa sun yi yadda suka ga dama saboda wasu daga cikinsu sun siya matsayin ne da makudan kudade.

“Bana sanya ran ganin wani abu, Najeriya za ta koma aya da kusan shekaru 100 da irin wadannan mutane a gwamnati. Masu adawa ba za su iya yin komai ba saboda a tsarin damokradiyya, yan tsiraru na iya fadin ra’ayinsu, amma babu shakka masu rinjaye ne ked a ikon aiwatarwa.

“Babu abunda za su iya yi, za dai su iya Magana ne kawai kamar yadda nake yi, amma ba za a taba kula su ba."

Hakazalika, tsohon dan majalisan wakilai Alhaji Nasiru Garba Dantiye, wanda har ila yau yayi hira a wayan talho, yace batun ‘rusunawa a wuce’ a lokacin tantance ministocin ya zamo abun damuwa.

Ya bayyana cewa irin tantancewar da yan Najeriya suka shaida ba shi bane ke tsare a kundin tsarin mulkin kasar ba, inda ya kara da cewa: “A ra’ayina, ba zancen rusunawa kawai a tafi bane saboda dangantakar dake tsakanin wadanda aka nada da kuma shugabancin majalisar dattawa.”

KU KARANTA KUMA: 'Yan Indiya sun fara marhaban da zuwan El-Zakzaky

Yace da ana bin ka’ida da ba a samu matsala irin na tsohuwar minister kudi, Kemi Adeosun ba wacce aka tantance a tare da satifiket din NYSC ba.

Sannan yace kamata yayi ace sanya kowani minista da mukamin da zai rike wanda yayi daidai da fannin da yak ware idan bah aka ba za a samu matsala.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel